Dakatar da Rahama Sadau ya haifar da cece-kuce
Tun bayyana da Kwamitin ladaftarwa na kungiyar ’yan fim ta MOPPAN ya dakatar da fitacciyar jaruma Rahama Sadau tsawon wata shida kan cin mutuncin Adam A Zango da ta yi a ranar Larabar makon jiya, a yanzu al’amarin ya haifar da cece-kuce, inda wadansu suka bayyana hukuncin ya dace, wadansu kuma suka ce bai dace […]
Tun bayyana da Kwamitin ladaftarwa na kungiyar ’yan fim ta MOPPAN ya dakatar da fitacciyar jaruma Rahama Sadau tsawon wata shida kan cin mutuncin Adam A Zango da ta yi a ranar Larabar makon jiya, a yanzu al’amarin ya haifar da cece-kuce, inda wadansu suka bayyana hukuncin ya dace, wadansu kuma suka ce bai dace ba.
A lokacin da kafar sadarwa ta Kannywoodscene ta tuntubi darakta Aminu Saira kan hukuncin da kwamitin ya yanke wa jarumar sai ya ce “Akwai kuskure, ya kamata a ce MOPPAN ta yi la’akari da hakurin da Rahama Sadau ta bayar, idan har Allah Zai karbi tubanmu, sannan Ya yafe mana, me ya sa MOPPAN ba za ta yi haka ba?”
Daraktan ya bayyana dakatar da Rahama kamar dakatar da furodusoshi ne, ya ce ya kamata MOPPAN ta tattauna da furodusoshi kafin ta yanke wannan hukunci.
Umar kofar Mazugal furodusa ne a kamfanin UK Entertainment ya ce MOPPAN ba ta kyauta ba, ta kuma nuna son kai, inda hukunci ba zai haifar wa industuri da mai ido ba.
“Rahama ita ce za ta ja ragamar fim dinmu mai suna ‘kasata’, amma a yanzu MOPPAN ta dakatar da ita, bayan mun kammala shiri. Yaya za a yi ke nan?”
Shi ma Darakta Yaseen Auwal bai amince da hukuncin da aka yanke wa jarumar ba, inda ya bayyana: “Idan har za a dakatar da Rahama, to ban ga dalilin da ba za a dakatar da Ali Artwork ba, saboda laifi iri daya suka aikata.”
Hassan Ibrahim mai sharhi ne a kan harkar fina-finan Hausa ya bayyana wannan hukuncin ya yi daidai, domin dole sai an tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.
“Wanna hukuncin ya yi daidai, domin ba wannan ne karo na farko da aka taba samun jarumar da aikata laifi makamancin irin wannan ba, idan ba a manta ba ta taba cin mutuncin marigayi Darakta AGM Bashir, kwamitin ya gayyace ta, inda ta rubuta takardar bada hakuri da alkawarin ba za ta sake aikata laifin irin wannan ba. Ga furodusoshi da daraktocin da suka ki amincewa da wannan hukuncin kuwa su za su kwana ciki, domin tuni kwamitin ya tura takardar dakatarwar ga Hukumar Tace fina-finai ta kasa da kuma ta Jihar Kano, idan sun kai fim dinsu wanda jarumar take ciki don a tace, to su ma sun san sauran.” Inji shi.
daya daga cikin mamban kwamitin ladaftarwar Isma’il NaAbba Afakallah sai ya ce “Ba wannan ne lokaci na farko da jarumar take cin zarafin abokan aikinta ba, ba za mu zura mata ido ta ci gaba da yin abin da ta ga dama ba tare da hukunci ya hau kanta ba. Dangane da Ali Artwork kuma wannan ne karo na farko da aka taba samunsa da aikata laifi irin wannan, ya amince da laifinsa, kuma ya yi alkawarin ba zai sake ba.”
Afakallah ya ce duk wani wanda yake da kwantiragi da jarumar ya rubata wa kungiyarsu korafinsa, za su samar da mafita dangane da al’amarin.
Da aka tambaye shi me ya sa kwamitinsu mata kawai yake ladaftarwa sai ya ce “Wannan ba gaskiya ba ne, mun taba ladaftar da Adam Zango.”