Dakatar da shi: Lamido Sanusi ya hadu da cikas a kotu

Wata Kotun Tarayya ta Abuja ta ce ba ta da hurumin sauraron karar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi ya shigar a gabanta, kan dakatar da shi da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi daga mukaminsa.Kotun ta ce batu ne da ya shafi ma’aikaci da ubangidansa, don haka ta mika lamarin gaban […]

Dakatar da shi: Lamido Sanusi ya hadu da cikas a kotu
Dakatar da shi: Lamido Sanusi ya hadu da cikas a kotu

 Sanusi Lamido SanusiWata Kotun Tarayya ta Abuja ta ce ba ta da hurumin sauraron karar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi ya shigar a gabanta, kan dakatar da shi da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi daga mukaminsa.
Kotun ta ce batu ne da ya shafi ma’aikaci da ubangidansa, don haka ta mika lamarin gaban kotun da ke sauraren kararakin al’amuran da suka shafi kwadago.
Malam Lamido Sanusi ya garzaya kotun ne yana neman ta fayyace masa ko Shugaba Goodluck Jonathan yana da ikon dakatar da shi daga mukaminsa na Gwamnan Babban Bankin Najeriya ba tare da tuntubar Majalisar Dokoki ta Tarayya ba.
A cikin watan Fabrairun bana ne Shugaba Jonathan ya dakatar da Lamido Sanusi daga mukaminsa bisa zargin ya saba ka’idar aiki.