Dakatar da shirin Ruga  bai ba mu mamaki ba – Sale Bayari

Alhaji Sale Bayari  shi ne Shugaban Kungiyar Ci-gaban Fulani ta Gan Allah ta Nijeriya, a tattaunawarsa da Aminiya ya ce ba su yi mamakin matakin da  gwamnati ta dauka na dakatar da shirin samar da Ruga ga Fulani Makiyaya ba. Ya ce ta kawo shirye shirye guda 3  irin  na Ruga, amma ta dakatar da […]

Dakatar da shirin Ruga  bai ba mu mamaki ba – Sale Bayari

Alhaji Sale Bayari, Shugaban Kungiyar Fulani ta Gan Allah

Alhaji Sale Bayari  shi ne Shugaban Kungiyar Ci-gaban Fulani ta Gan Allah ta Nijeriya, a tattaunawarsa da Aminiya ya ce ba su yi mamakin matakin da  gwamnati ta dauka na dakatar da shirin samar da Ruga ga Fulani Makiyaya ba. Ya ce ta kawo shirye shirye guda 3  irin  na Ruga, amma ta dakatar da su saboda adawar da wadansu ’yan Najeriya suke yi:

A matsayinka na daya daga cikin shugabannin Fulani makiyaya a Najeriya, me za ka ce kan matakin da gwamnati ta dauka, na dakatar da shirin Ruga?

A wurina wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka ba wani abin mamaki ba ne. Domin na san a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan,  an yi  taron kasa   a shekarar 2014,  inda aka duba matsalolin al’ummar Najeriya. Na san  a wajen taron, an bayar da shawarar cewa a hana Fulani makiyaya kiwo irin na gargajiya, wayo yawo da dabbobi. Na san a lokacin ba a tabbatar da wannan doka  ta  hana  kiwo ba.

Amma da zuwan wannan gwamnati a shekarar 2015,   karkashin Ministan Gona Cif Audu Ogbeh sai  aka fara kiranmu ana gaya mana cewa, kiwon nan na gargajiya da Fulani makiyaya suke tashi daga nan zuwa can ba zai yiwu ba. Domin wai  yana kawo rikici a tsakanin Fulani makiyaya da manoma. Sai aka ce mana yanzu ana son a koma makiyaya irin ta da, wato Grazing Reserbes. Kuma shi wannan shiri na  Grazing Reserbes dama hankalinmu bai kwanta da shi ba. Domin al’ummar Fulani makiyaya mutane da suka saba da   kiwo na gargajiya, don haka  lokaci daya ba zai yiwu a kira su a killace su a wuri daya ba. Amma duk da haka muka jawo ra’ayinsu, daga baya muka samu wadanda suka ce sun amince,  a gwada a gani. Kafin a gwada wannan tsari, sai muka ji cewa manoman Najeriya sun ce ba su yarda  da wannan tsari ba, suka ce wadannan filaye na Grazing Reserbers  gonakin wadansu mutane ne.

Daga nan sai aka ce wannan shiri ba zai yiwu ba, don haka bari a koma wani tsari na  wuraren kiwo mai suna Ranches, muka ce ba mu ki ba, ba mu yarda ba, amma  bari mu gani tukuna wato mu ga kamun ludayin gwamnati kan wannan shiri. Aka je aka kawo wata ciyawa daga kasar Barazil aka ce ita ce za a rika shukawa a wannan shiri na Ranches ana ciyar da shanu, wannan ma ya gagara.

Aka dawo aka bari aka ce bari a koma wani shiri  na manyan gandun kiwo wai  shi Cattle Colony.  Kafin a ce haka sai wadasu ’yan Najeriya suka ce ba su yarda da wannan shiri ba. Wato  a cikin shekara hudu an kawo mana abubuwa guda uku, amma babu daya da aka yi.

Duk gwamnatin da za ta yi wani abu na kare rayuka da lafiyar mutanen Najeriya, dole ne ta dubi al’ummar Fulani makiyaya na Najeriya. Domin mu ma mutane ne da muka kai sama da mutum miliyan 20 a Najeriya, kuma dukiyarmu ta shanu da ita ce muke ciyar da al’ummar Najeriya da nama. Don haka idan har wadansu za su ce kada gwamnati ta kula da mu, wannan ya zama wani babban bala’i a Najeriya.

Kuma yanzu muna ganin watakila lokaci ya zo da za a samu mafita ta hanyar fito da wannan shiri na Ruga wanda shi ma ba mu san shi ba. Muna  kokarin mu san mene ne ake nufi da wannan shiri. Sai kuma muka fara jin wadanda suke adawa da duk wani abu da aka ce za a yi wa Fulani makiyayi a Najeriya, suna cewa ba su yarda ba. Sai muka ce  mu babu abin da za mu ce, sai dai mu zuba ido mu gani.

Daga nan abin bakin ciki yanzu sai aka zo aka ce wai wadanda suke adawa da Fulani makiyayan nan wadanda ba sa son su rayu a Najeriya su ne suka yi nasara. Don haka wannan gwamnati ta dakatar da wannan shiri na Ruga.

Wannan abin bakin ciki ne kwarai da gaske. Don haka mu yanzu mun gano cewa  a Najeriya babu kiwon gargajiya babu kiwon hurumi babu kiwon Ranches babu kiwon Colony, babu kiwon Ruga. Don haka muna hangen cewa kafin  wannan gwamnati ta kammala wa’adinta, mai yiwuwa ne a rasa Fulani makiyaya a Najeriya.

 

To amma wadansu ’yan Najeriya suna ta sukar wannan gwamnati, cewa tana son ta mayar da kasar nan kamar ta Fulani makiyaya  ce kadai?

A yadda Najeriya take babu wani mutum da za a ce don yana Shugaban Kasa kuma yana da ministoci da jami’an tsaro da ma’aikata daga kowace jiha a Najeriya, sa’annan a ce wai zai mayar da wannan kasa ta wata kabila guda daya. Ni ina ganin wannan wani shaci-fadi ne kawai kuma mummunar magana ce da ake yi don a bata wata kabila, domin a samu hanyar da za a tauye mata ’yanci.

Kuma a karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya al’ummar Fulani makiyaya suna da hakki kamar yadda kowanne dan Najeriya ke da shi. Amma ana nuna mana cewa ba za ta yiwu al’ummar Fulani makiyaya su rayu a Najeriya ba, wannan ba karamin bala’i ba ne.

Dole ne wannan gwamnati ta daina bari ana gaya mata abin da za ta yi, da abin da ba za ta yi ba. Saboda  babu abin da gwamnati za ta yi, wanda zai kasance jama’a su goyi baya 100 bisa 100.

Saboda haka ina ganin lokaci ya yi da za a tsaya a duba shin  a kasar nan, akwai mutanen da za a fitar da su daga kasar ce,  saboda su Fulani ne ko don su ’yan Arewa ne?.

 

Ganin yadda irin wadannan  abubuwa suke tafiya  a zamanin wannan gwamnati, kana ganin cewa za a yi wani abu da zai kawo karshen matsalolin al’ummar Fulani makiyaya kuwa?

To ni dai na san ana cewa Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake ganewa. Don haka ni dai maganar harkar Fulani makiyaya a wannan gwamnati, babu abin da zan ce maka zai yiwu, ko ba zai yiwu ba. Domin na ga an yi maganar shirye-shirye har guda hudu, amma babu daya da ya yiwu. Don haka a wurina  babu wani abu guda daya ko biyu da za a ce zai yiwu in yarda. Mu yanzu Fulani makiyaya a zamanin wannan gwamnati sai yadda aka juya mu. Ba mu da ta cewa, duk da cewa babanmu  kuma danmu ne yake mulkin Najeriya. Ba mu ce  ya ki wadansu ’yan Najeriya ya ce mu kadai yake so ba. Amma kuma ya kamata ya san cewa mu ma Fulani makiyaya muna da hakki a Najeriya, kamar yadda kowane dan Najeriya ke da hakki. Don haka ko wa yake mulki ya zama wajibi ya bai wa kowane dan Najeriya hakkinsa.

To, ina mafita kan wannan lamari?

Ni ina ganin yanzu abu daya ne ya rage, wato  ina rokon Shugaban Kasa da gwamnatin Najeriya wannan abu da yake  son ya fi karfin kowa a Najeriya,  Shugaban Kasa ya nemi fitattun mutane a Najeriya masu fada-a-ji da wadanda suke adawa da duk wani abu da aka ce za a yi wa Fulani makiyaya na kyautata rayuwarsu a Najeriya,  a yi wata zama a dubi wannan magana ta Fulani makiyaya a Najeriya. A fadi yadda za a yi da Fulani makiyaya a Najeriya.