Dakatar da shirin Ruga kuskure ne babba
Bayan gaisuwa da fatan alheri, a yau na shigo wannan gida ne domin yin tsokaci game da dakatar da shirin samar wa Fulani Makiyaya rugagen kiwo na musamman da gwamnatin Najeriya ta yi, sakamakon nuna adawa da shi ƙarara da waɗansu daga cikin gwamnoni da ɗaiɗaikun mutane suka yi a Najeriya. A zahirin gaskiya ko […]
Bayan gaisuwa da fatan alheri, a yau na shigo wannan gida ne domin yin tsokaci game da dakatar da shirin samar wa Fulani Makiyaya rugagen kiwo na musamman da gwamnatin Najeriya ta yi, sakamakon nuna adawa da shi ƙarara da waɗansu daga cikin gwamnoni da ɗaiɗaikun mutane suka yi a Najeriya.
A zahirin gaskiya ko kaɗan bai dace gwamnatin Najeriya ta dakatar da wannan shiri ba saboda nuna adawa da shi da wadansu da za mu iya kira da tsirari suka yi, kasancewar babu wani abin alheri da za a aiwatar ba tare da wadansu sun nuna adawa a kansa ba don kawai wata buƙata ta ƙashin kansu.
Idan muka yi la’akari da yadda rikicin manoma da makiyaya ya ƙasaita har ya rikiɗa ya koma ta’addancin da yake neman ya tarwatsa yankinmu na Arewa, ya zama wajibi Shugaba Buhari a matsayinsa na ɗan Arewa ya yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya kawo ƙarshen wannan matsala kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa. Domin idan bai daƙile wannan ta’asar da ke faruwa a yankinmu na Arewa ba to wa yake tunanin zai zo ya kawar da wannan ta’addanci?
Mai girma Shugaban Kasa ya kamata ka yi amfani da madubin duba rudunka game da waɗanda ke adawa da wannan shiri, domin babbar fa’idar wannan shirin na farko zai kawo ƙarshen satar shanun jama’a, domin dama idan aka saci shanun daji ake shigewa da su a ɓatar, to idan kuwa an samar da rugage keɓantattu to ta yaya ɓarawo zai yiwo satar shanu ya iya hallakar da su cikin sauƙi?
Na tabbatar mafi yawan gwamnonin Arewa da Fulanin duk sun aminta da wannan shiri, to ta yaya wadansu gwamnonin Kudu su da wasu tsirarin ’yan Arewa da ba a san halayya da manufofinsu ba, adawarsu tasa a dakatar da wannan shirin da ake tunanin zai haifar da wanzuwar zaman lafiya a yankinmu na Arewa?
A ƙarshe Mai girma Shugaban Kasa idan har babu damar yin waɗannan rugage a matakin tarayya, to muna roƙo ka bai wa duk wani Gwamna da ya aminta da wannan shiri damar samar da waɗannan rugagen a jiharsa, domin ka sani akwai tarin mutanen da suka haɗa da ’yan Kudu da ’yan Arewa waɗanda ba sa fatar karewar waɗannan tashe-tashen hankula a Arewa domin kawai wata buƙata ta ƙashin kansu!
Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan-Ɓaure (Ɗan kishin talaka), Zamfara, Najeriya.
08139177665