Dakon kaya da jaki na neman bacewa a kasar Hausa – Kasimu Mai Manya
Aminiya ta zanta da wani mai sana’ar dakon kaya da jaki wanda ya dade yana wannan sana’a, inda ya ce sana’ar na neman zama tarihi duk da cewa akwai rufin asiri a cikinta: Aminiya: Kamar shekara nawa ka fara dako da jakuna? Kamar yadda na fadi sunana Kasimu Umar amma an fi sanina da Jawo […]
Aminiya ta zanta da wani mai sana’ar dakon kaya da jaki wanda ya dade yana wannan sana’a, inda ya ce sana’ar na neman zama tarihi duk da cewa akwai rufin asiri a cikinta:
Aminiya: Kamar shekara nawa ka fara dako da jakuna?
Kamar yadda na fadi sunana Kasimu Umar amma an fi sanina da Jawo Mai Manya wato Mai Jakuna, kuma na yi kusan shekara 20 ina dakon kaya da a kan jakuna. Ba gado na yi ba, sai dai na bi masu aiki da jakuna na tsawon lokaci kafin in fara cin gashin kaina, don haka tun ina dan shekara goma sha daya na fara aiki da jaki har zuwa yau sana’ata ke nan.
Aminiya: Mene ne bambancin aiki dako da jaki a da da yanzu?
To a gaskiya yanzu sana’ar ba kamar da ba, domin a da kowane irin kaya za a kira ka domin ka dauka, kuma ka kai ko’ina, amma yanzu yawaitar ababen hawa na zamani kamar su babura da kananan motoci su ne suke neman dakile harkar daukar kaya da jaki ko da a kauye ne kuwa. Ka ga misali da idan ana cin kasuwa mu ne masu daukar kaya a kauyuku da gonaki mu kai kasuwa, sannan daukar taki zuwa gona.
Shekaru kadan nan baya da suka wuce akwai kauyen da a lokacin ina yaro har amarya da kayanta a jaki ake dauka a kai ta dakin mijinta. Amma a yazun wace amarya ce za ta yarda ta hau maka jaki komai kauyancin gari?
Ni kaina ina yaro yana daga cikin abin da ya ja ra’ayina har na fara bin masu jakuna, wato daukar amarya da ake yi a jaki a kai ta dakin miji.
Tunda ni ba gado na yi ba, to ka ga yanzu ko kayan da ake kaiwa kasuwa ba a cika kiranmu mu dauka ba, idan dai kayan ba na mai jakin ba ne. Yanzu yawancin aikin da muke yi da jakuna shi ne dakon kasa da yashi, da kai taki gona, amma a da za a kira ka ka zo ka dauki doya ko hatsi da gyada da sauransu. Amma yanzu sai dai babura da motoci ke dauka.
Aminiya: A wace kasuwa kuke samun jakuna?
Muna samun su ne a kasuwannin Katsina da kasar Nijar har yanzu can muke zuwa mu sayo. Kuma da za ka iya samun jaki mai kyau a kan kudi Naira dubu 18 ko dubu 20, yanzu kuwa sai kana da Naira dubu 80 kafin ka samu jaki mai kyau kuma duk da koma-bayan sana’ar.
Kuma idan kana kula da jakinka, za ka dauki tsawon shekara kusan bakwai zuwa takwas kana aiki da shi kafin ka sake wani, domin idan ya fara rauni akwai masu saye, su kuma suna kai wa yankin Kudu maso Gabas inda ake cin namansa.
To amma yanzu mun samu labarin cewa wai Turawa na sayen jakunan suna amfani da shi.
Aminiya: Kana da jakuna kamar nawa yanzu, kuma kana daukar awa nawa kana aiki da su kafin su huta?
Ina da jaki guda biyar, kuma ina daukar akalla tsawon awa biyar muna buga aiki idan akwai aiki, sai dai muna tsayawa na dan wani lokaci mu huta.
Aminiya: Kana iya samun kamar nawa a rana?
Idan Allah Ya kawo kasuwa ina hada Naira 4,000 wani lokaci 5,000 kai har ma ina fin haka idan aikin kusa ne.
Aminiya: Wane irin abinci kake ba su, kuma suna cin nawa a kullum?
Ina ba jakuna buntun shinkafa amma ina hada musu da dawa. Hikimar hada musu da dawa ita ce domin yana kara musu karfi da kuma gabobin jiki, domin irin kayan da suke dauka, kamar kasa da sauransu. In kana ba su dawa to za su dade da karfi a jikinsu, sai kuma da daddare ina ba su karan dawa da sauransu su kwana suna kiwo domin idan gari ya waye ka ga ba tsayawa sai tafiya aiki kawai.
Aminiya: Wane irin rufin asiri ka samu a cikin sana’ar dakon kaya da jaki?
A gaskiya na samu rufin asiri da dama da wannan sana’ar domin na auri mata biyu, kuma na gina gida, na sayi gonaki da nake noma.
Kuma yadda nake jin dadin sana’ar nan zai yi wuya in bar ta domin ina samun rufin asiri a cikinta ba kadan ba, sai wanda yake irin sana’ar ne zai iya gane haka.
Aminiya: Ko kana da wata shawara da za ka ba masu zaman banza?
Ina kira ga matasa da su tashi wajen neman na kansu domin su kare mutuncinsu. Kuma su daina kyama ko jin kunyar sana’a domin ba a jin kunya da yunwa ko rashi. Sakona ke nan.