Dala miliyan 44 ta yi batan-dabo a lalitar hukumar NIA
Watanni biyu bayan sallamar tsohon darakta janar na hukumar leken asiri ta Najeriya, Ambasada Ayodele Oke kuma kwanaki biyu kafin nadin Ahmed Rufa’i Abubakar a matsayin sabon daraktan hukumar wata almundahana ta sake kunno kai a hukumar a cikin makon da ya gabata inda aka kwashe tsabar Dala miliyan 44 daga lalitar hukumar aka kai […]
Watanni biyu bayan sallamar tsohon darakta janar na hukumar leken asiri ta Najeriya, Ambasada Ayodele Oke kuma kwanaki biyu kafin nadin Ahmed Rufa’i Abubakar a matsayin sabon daraktan hukumar wata almundahana ta sake kunno kai a hukumar a cikin makon da ya gabata inda aka kwashe tsabar Dala miliyan 44 daga lalitar hukumar aka kai su wani wuri na daban.
Wata majiya daga manyan jami’an hukumar ce ta tseguntawa Aminiya lamarin inda ta ce tuni aka kwashe kudin tun kafin sabon shugaban hukumar ya kama aiki.
Majiyar ta bayyana cewa gwamnatin shugaba Jonathan ta saki Dala miliyan 260 ga hukumar NIA a matsayin kudin agajin gaggawa to amma lokacin da gwamnatin tarayya ta kaddamar da bincike kan kudin a shekarar da ta gabata aka gano makudan kudin a Legas da kuma tsabar Dala miliyan 44 wadanda aka ajiye a asusu na musamman na hukumar da ke Abuja.