Dala miliyan 462 da gwamnati ta fitar ya saba wa doka-Majalisa
Majalisar Dattawa ta aike da sammaci ga ministan kudi da na tsaro da kuma babban gwamnan bankin Najeriya na CBN kan zargin fitar da Dala miliyan 462 ba bisa ka’ida ba daga asusun gwamnatin tarayya. Ana sa ran Ministan kudin, Kemi Adeosun da Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali da gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, […]
Majalisar Dattawa ta aike da sammaci ga ministan kudi da na tsaro da kuma babban gwamnan bankin Najeriya na CBN kan zargin fitar da Dala miliyan 462 ba bisa ka’ida ba daga asusun gwamnatin tarayya.
Ana sa ran Ministan kudin, Kemi Adeosun da Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali da gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Godwin Emefele za su gurfana a gaban kwamitoci daban-daban don amsa tambayoyi kan batun a mako mai zuwa.
Sanata Sam Anyanwu dan jam’iyyar PDP daga jihar Imo ya ce a wani kuduri cewa an fitar da kudin ne ba tare da amincewar majalisar tarayya ba.
Ya ce “A watan Maris na shekarar 2018 gwamnatin tarayya ta fitar da Dala miliyan 462 daga asusun gwamnatin tarayya. An biya wani kamfanin kasar Amurka don ya sayo jirgi mai saukar-ungulu. An yi haka ne ba tare da amincewar majalisar dattawa ba da kuma ta wakilai. Na san babu wata bukata da aka da gwamnatin tarayya ta kawo don neman amincewar fitar da kudin”.