Dala na ba Shata ya yi mini waka – Inuwa dalibi

Bawan Allah Inuwa dalibiMutumin kirki Inuwa dalibiMutumin Allah Inuwa dalibidanfalaki Inuwa dalibiAlheri dai Inuwa dalibiMai kaunar Allah Inuwa dalibi… Malam Inuwa dalibi, malami ne na makarantar allo, kuma ya shahara a wakar Shata mai taken “Bawan Allah Inuwa dalibi.” Don haka Aminiya ta garzaya unguwarsu can Kwanar diso cikin birnin Kano, inda ta tattauna da […]

Dala na ba Shata ya yi mini waka – Inuwa dalibi

Bawan Allah Inuwa dalibi
Mutumin kirki Inuwa dalibi
Mutumin Allah Inuwa dalibi
danfalaki Inuwa dalibi
Alheri dai Inuwa dalibi
Mai kaunar Allah Inuwa dalibi…

Malam Inuwa dalibi, malami ne na makarantar allo, kuma ya shahara a wakar Shata mai taken “Bawan Allah Inuwa dalibi.” Don haka Aminiya ta garzaya unguwarsu can Kwanar diso cikin birnin Kano, inda ta tattauna da shi kan yadda suka hadu da Alhaji Mamman Shata har ya yi masa waka. Ya bayyana wasu al’amura da suka shafi tarihin rayuwarsa, musamman yadda ya yi aikin masinja a gidan Gwamnatin Kano, tun daga zamanin mulkin Gwamna Stephen Shekari zuwa Kwankwaso karon farko, sa’adda aka yi masa ritaya. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ko za ka ba mu takaitacccen tarihin rayuwarka?
Malam Inuwa dalibi: Bismillahir Rahamanir Rahim, Allah Ka ba mu fahimta kan wannan magana da zan yi game da Alhaji Mamman Shata. Haduwata da Alhaji Mamman Shata, Allah Ya gafarta masa, Allah Ya sa mu kuma mu cika da imani.  A lokacin da nike zuwa wajen Alhaji Mamman Shata, zan fadi dan takaitacce ne kadan. Idan an ce Shata zai yi wasa a Neja ko a Kissgadi (King’s Garden), a wancan lokacin nakan je ina sauraro a waje, wani lokaci sai yara suka zo suka ce kai dalibi Shata yana can yana waka yana cewa duk wanda ya ba shi kaza, wato Dala zai yi masa waka. Kasan Dala kuwa a wancan lokacin kudi ne sosai. To ina da daloli, lokacin nan ina ciniki; dalullukan (daloli) ga su nan ina da su, sai na samu wajen dala ko 50 ne wadanda ba su fi Fam 20 ba, sai na ba Alhaji Bala kofar Na’isa, maroki, na ce, ‘ga naka Dala daya, Shata kuma ka ba shi Dala biyar, amma ni ne Inuwa dalibi a Kwanar diso, in na ji waka ta yi dadi zan kara masa Dala 50. Shi ne fa. Duk sa’adda na je wurin Shata in na fara bayar da kudi har karba ake yi. Wannan lokaci na san cewa Shata ya san lokacin da nike zuwa wajensa.
In na hau kan kekena, sai in tafi wajensa. A lokacin ma ba a yi wakar ma ba. Idan na je gidansa a Kurnar Asabe, ya fito daga kofar gida, sai ya zauna, yana kan kujera, a dauko masa furarsa; ta ji irin kindirimon nan ya juyata ya sha. Kuma ya sa a sawo danwake, a ce za a ci. Ina waje daya ban taba cewa nine wane ba; a lokacin ma fa ba a yi wakar ba. To, tun daga wannan lokacin in na zo sai in kawo ko Fam daya ko biyu in ba yaransa idan na tashi tafiya. Ka ji yadda aka yi na fara zuwa wajen Shata, na fara bayar da wadannan kudi.
Wata rana Shata na wasa a Neja Kulob, sai ya yi mini waka, su kuwa ‘yan kallo suka ce ba su ga wanda ake yi wa wakar ba. Ka ji yadda aka yi na je Neja kulob aka ganni. Sai kuma saádda aka sanar da ni cewa, Shata ya tafi daji can bakin ruwa a Tiga Dam yana yi mini waka.
Aminiya: Kamar nawa ke nan ka bai wa Shata?
Malam Inuwa dalibi:Ai na dade ban daina bayar da kudi ba.Kai har mutane na ganin cewar kamar shi Shata ke ba ni kudi. Ai Shata ban daina ba shi kudi ba har sai lokacin da aka ce ya kwanta a asibiti. A asibitin can waje. To, shi ne Malam Iliya yaronsa ya ce Dokta fa yana asibiti. Lokacin shi ne na yi sallar La’asar a Masallacin Juma’a ban tsaya ba, saboda an fada mini cewa Dokta ba shi da lafiya.Ka san duk lokacin da Shata ya zo garin nan zai yi wasa sai an fada mini. To da na yi sallar La’asar, na ce to zaman me zan yi,bayan na yi lazami, na yi wuridi in tafi asibitin mana, sai na hau kekena sai can asibitin da ya kwanta, ina zuwa sai hadari ya taso, ni kuwa na ce oho dai, ni dai ba zan fasa ba, sai da na shiga asibiti. Sai na tambayi inda Dokta yake, sai aka ce ai ga dakin can. Na shiga, ina kallonsa, yana kallona, kamar ya ce Malam Inuwa. Na zaga bayansa,na ce, to Allah Ya ba shi lafiya. Ina fitowa ina jin iyalansa suna shiga ciki. Suna jan wannan adaka tasu a kasa, sannan na dawo. Ban san cewa, an dauke shi daga wannan waje ba, domin cikin wannan dare ya rasu aka kai shi Daura.
Aminiya:  Za mu so mu ji haduwarka da Alhaji Mamman Shata shekara nawa?
Malam Inuwa dalibi: Shekarun suna da yawa. Ni ban san yawan shekarun ba, tun da kai ka zo har nan, don babu wani dan jarida da ya taba hira da ni a kan irin wannan, amma akwai lokacin da aka kai ni Kazaure za a yi hira da ni a gidan rediyo, sai na kama zazzabi. A haka dai aka yi hirar nan.
Aminiya: Wai wane Sarki ke mulki a Kano zamanin da kuka hadu da Alhaji Mamman Shata?
Malam Inuwa dalibi: Lokacin da muka hadu da Alhaji Mamman Shata, Sa Muhammadu Sanusi ke mulki a Kano. Ka san lokacin Shata ya yi wa karuwai waka, ya ce sun taru, sun yi jugun-jugun. Lokacin da Sarkin Kano Muhmmadu Sanusi ya yi wa ’ya’yansa aure, sai in aje kwaryar bara, idan na je na yi Allazi wahidin, aka ce Shata zai yi wasa, sai in je in makale ina sauraro. Da Sarki Sanusi zai aurar da ’ya‘yansa, da Shata ya fara wasa, ban baro wurin nan ba, tun karfe 8 ko 10 na dare sai Asuba, kai sai da Shata ya tashi.
Aminiya: Allah Ya gafarta Malam Shekarunka za su kai nawa?
Malam Inuwa dalibi: Ai na wuce 60. akwai lokacin da na dawo bara, aka ce Shata zai yi wasa a kofar Kudu, har shi ma ya fada cewa rabonsa da roko a wannan gidan ko shekara 20 ko nawa ne? A lokacin ma ban san za a yi min waka ba.
Aminiya: Wane ne sanadiyyar haduwarka da Alhaji Mamman Shata?
Malam Inuwa dalibi: Zuwa kawai nike yi wajensa. Ai in kana son mutum ba sai an ce ga wani ya sada ka da shi ba. Idan aka ce da wani maroki za ka daura auren ’yarka, ai ba sai ka ce kaza-kaza ba, zuwa kawai zai yi.
Aminiya: Za mu so jin irin daukaka ko fa’idar da wakar Shata ta jawo maka?
Malam Inuwa: Ai ni yadda nike son wakar Shata, ga zato na dai, kai! Sai dai wakar Hamisu, wanda Shata yake cewa ya hana banjo da kukuma ya hana Hamisu, to ina son wakar Hamisu. Akwai lokacin da na hadu da Alhaji Ummaru dan danduna na Gwandu, a wurin da ake yi mana recording na kaset ya tambaye cewa, a lokacin da Alhaji Sani Buhari Daura zai aurar da ’ya’yansa Shata yana wasa.
Akwai lokacin da Shata yake cewa,”Bawan Allah Inuwa dalibi, yara sun ce nasu ne, manya sun ce nasu ne.” wani a nan gidan Falaki, ya mike Shata na wasa, ya ce a fada wa Shata ai Inuwa namu ne. Alhaji Aminu Falaki. Akwai lokacin da Gwamna Wase, wanda jirgin sama ya fadi da shi, sojan nan, sai ya aiko daraktan  sashen tarbar baki da shirya girke-girke zuwa wurin Shata. Sai ya ganni ina gaban Shata. Masinja ne ni fa.Sai suka tsaya a gaban Shata, sai wannan ya dubi wannan, wancan ya dubi wannan. A wancan lokacin dama da na taso daga gidan gwamnati sai in canja yunifom, in sanya kayana, in dan fesa turare, sai in tafi wurin Shata. Da suka ganni tare da Shata sai suka tsaya bakin kofa.ina kallonsu. Sun dade suna tsaye, sai suka shigo, suka ce ranka ya dade aiko mu aka yi. Suka fadi irin mukamin nan da ake yi wa shugabanni, suka ce gwamna ne ya aiko mu, yana nemanka. Sai Shata ya ce da ni, Malam Inuwa, an aiko Gwamna yana nemana. Sai suka tashi suka tafi, za a je a hada ni da manya. Lokacin nan Adda’u da wani duk manya ne a gidan gwamnati. Shi Adda’u da nike fada, wato shi ne direba na Protocol. Ashe su mamaki na suke yi. Don akwai wani mutum Baba Audi, Allah Ya jikansa, ya ce mini, kai Malam Inuwa lokacin da kake tafiya wajen Shata ba ka fada mini ko? Shi ya sa kake tafiya kai kadai. Ka fada mini mana mu rika zuwa tare.
Kuma akwai Ibrahim Na Habu, shi ma Allah ya yi masa rasuwa. Sai ya ganni a gaban Shata, ya ce Allah Sabninani tafiya zan yi. Lokacin nan wakar ta rabu da shi. Ni dai na ganshi da wata ’yar shara ya taho ya tsugunna, ya ce mini ka gode wa Allah, ka gode wa mutumin nan. Saboda irin yadda ya yada ka a duniya. Lokacin fa zan tashi, kana ji ko? Sai ya ce, halin malantar za a yi mana? Ina da Naira 200, sai na ciro na ba shi, sai ya ce ai haka ake yi.
Aminiya: Dama ka yi aiki a gidan gwamnati ne?
Malam Inuwa dalibi: Eh, na yi masinja, tun lokacin Gwamnan Kano Stephen Shekari, kuma sai da Kwankwaso ya zo, zuwansa na farko, ba wannan ba, ya yi mini ritaya. Kuma a lokacin Stepehn Shekeri har nuna ni ake yi a gobernment house, wai ni ne wanda aka yi wa waka, har wani darakta ya rika tambaya, ko na yi kudi? Ba  su san cewa ni almajiri ne ba.
Aminiya: Malam Inuwa yaya maganar iyali fa?
Malam Inuwa dalibi: Ai ni mutumin Maigana ne, sai dai a gidan Falakin Kano aka san ni. Don haka da ’ya’ya da ’yan uwa duk suna cikin iyali. Da sun ji za su gane ni. Kuma ni da karatuna na zo Kano, domin Malamina da na yi karatu a kasar Zazzau a wajensa, shi ne Malam Uwaisu, a gaban gidan Mai martaba Sarkin Zazzau. Kodayake na yi makarantar Shehu Maihula. Shi ya kawo ni Kwanar diso, inda na zauna gidan wani Saje, babban soja ne, daga can kuma na koma gidan Falakin Kano. Falakin nan da Sarki Sanusi ya nada shi, kuma tun da ya rasu ba a sake nada wani ba.