Dala ta fado zuwa N750 a kasuwar bayan fage
Dalar takan kai N730, amma idan mai sayen na so a tura masa kudin ta asusu sun sa banki, sai farashin ya yi kasa zuwa N700.
Darajar Naira ta soma farfadowa a kasuwar canji inda ta koma 730 a kan Dala daya, bayan faduwar da ta yi mako biyu a jere.
Darajar Naira ya soma dawowa ne a hankali, wanda ya sa aka sayar da Dalar kan N730 a ranar Alhamis.
- Naira ta shiga jerin kudaden da darajarsu ta fi faduwa a duniya
- ‘Sake fasalin Naira zai sa ’yan bindiga su koma karbar kudin fansa da Dalar Amurka’
Masu canjin kudi sun danganta tashin darajar kudin ga karancin Naira a hannun masu son sayen Dala, wanda hakan ya sa ’yan canji ba sa iya kara kudin Dalar da za su sayar.
“Hakika akwai karancin Naira a kasuwar canji,” a cewar wani dan canji a hirarsa da Daily Trust a kasuwar canji da ke tsakiyar birnin Legas.
Dan canjin ya kuma ce, Dalar takan kai N730, amma idan mai sayen na so a tura masa kudin ta asusu sun sa banki, sai farashin ya yi kasa zuwa N700.
A Fatakwal wani dan canji a hirarsu da wakilinmu ya ce, yana da ita a N700, amma zai sayar da ita ne a N720 ga masu saye.
A hirar wakilinmu da wani dan canji a unguwar Zone 4 a Abuja, ya ce, “Mutane yanzu na tsoron sayen Dala ne saboda labarin da ake yadawa na cewa Amurka na kin karbar $100, don haka sayen ta ya zama hasara.”
Wani dan canjin kuma cewa ya yi, wasu daga cikin abokan sana’arsa na ganin cewa mutane sun koma sayen kadarori saboda tsoron yadda sake wasu takardun Naira da gwamnati zai shafe su.
Daga Yakubu Liman, Vincent Nwanm da Abiodun Alade