Dalalinmu na tursasa dokokin gudanar da kamfanonin waya – NCC
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce ta tilasta aiki da dokokin mulki ga kamfanonin waya a fadin kasar nan ddon tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu a wannan masana’anta, sannan a sake kwata darussan da aka koya daga sauran fannoni, wadanda suka yi fadin-tashin kwaramniyar ‘nasara da faduwa.’ Shugaban Hukumar Daraktocin NCC Sanata […]

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce ta tilasta aiki da dokokin mulki ga kamfanonin waya a fadin kasar nan ddon tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu a wannan masana’anta, sannan a sake kwata darussan da aka koya daga sauran fannoni, wadanda suka yi fadin-tashin kwaramniyar ‘nasara da faduwa.’
Shugaban Hukumar Daraktocin NCC Sanata Olabiyi Durojaiye a wajen taron tabbatar da dokokin harkokin mulki da aka gudanar a yankin Kudu maso Gabas ya bayyana a karshen makonnan da aka gudanar kan tabbatar da dokokin harkokin mulki a Enugu, a Jihar Enugu.
Ya ce hukumar ta tashi daga matakin ganin dam zuwa tilasta aiwatar da dokokin mulkin don ceto wannan masana’anta daga durkushewa, tare da bayar da kariya da dimbin jari da aka zuba da ayyukan yi.
Ya ce: “ Bayan da hukumar ta yi kyakkyawar ganawa da masu ruwa da tsaki, sai hukumar ta bayar da sanarwar fara aiki da tilast aiwatar da dokikin na harkokin mulkii ga masana’antar tun daga ranar 1 ga Nuwambar 20016. Bisa managarcin tsarin jan ragama al’amura, hukumar ta yi la’akari da da irin martanin da ta samu bayan da ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki kafin fara aiwatar da tilasta aiki da dokokin.
‘Jigon manufar kafar tattaunawar, ya ta’allaka ne kan yadda za a tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu a wannan masana’anta tare da kwata irin darussan da aka samu daga wasu fannonin da suka yi fafutikar hawa da sauka,” wanda kusan a iya cewa ba za a ce lallai yanzu ne ya fi dacewa ba. Manufar dai shi ne dai cimma manufa ta bai daya ga masu ruwa da tsaki a wannan masan’anta don tabbatar da tsarin gudanarwa da dorewar tsare-tsare, yayin da ake tallata dabarun kulla dangantaka a tsakanin rukuni-rukuni masu hada-hadar kasuwanci da daidaito wajen ayyukan kamfanonin waya.
‘An tursasa aiwatar da dokar ne duk da matsalar tattalin arziki da aka yi fama da ita, inda dimbin al’amura suka ahdu suka haifar da ita, wadanda suka hada da faduwar daraja man fetur, da matsalar cin hanci da rashawa da ta baibaye ma’aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, ga dimbin bashi da ya yi katutu a cikin gida da waje, sai karancin samun kudin shiga ga daidailku, sannan yawan shigo da kayayyaki sabanin fitar da su, al’amarin da ya haifar da matsala wajen daidaita tsarin kasuwanci da haeda-hadar kudi ta duniya, ga dimbin kudin da aka kashe wajen gyara dimbinm barnar da rikicin Boko Haram ya haifar a amtsayin kalubalen da ya baibaye yankin Arewa maso Gabas ta tsakiya, inda aka samu kwarancin kayan more jin dadin rayuwa, sannan ga tashin0-tsashinan yankin Neja-Dalta.. Nan da zuwa yulin 2018 tursasawar hauhawar farashi sanadiyyar gurbatacciyar hada-hadar juya kudi a cikin kasa, al’amarin da ya yi matukar gurgunta tattalin arziki.
Ya ce a matakin kamfanonin wayar sadarwa. Yanayin ya yi muni. A zahiri suna nuna kyakkyawan yanayi kan gudunmuwarsu wajen bunkasa hada-hadar dukiya a cikin kasa, ta yadda ake kimantawa da Naira tiriliyan guda da biliyan 400 a kowane wwatanni uku cikin shekarar 2016 a daidai lokacin da tattalin arziki ke tangal-tangal.
Ya ce alamu sun nuna ba su jigata ba in an yi nazarin turakun juya akalar bunkasar tattalin arziki.
‘sai daia cewar Ministan farko na kasuwanci da masana’antu a Najeriya, Alfred Chuchukwu Nwapa ya taba cewa,’ ba za ka taba kasancewa a cikin jirgin ruwan da ke tangal-tangal ba a ce kai ma ba ka tangal-tangal din kifewa ba, inda kyakkyawan nazari na nuni da cewa wannan masana’anta tana hawa ne da sauka a hankali, a hankali daga shekara zuwa shekara, inda dimbin Abin da ake samu a wajen kowane mai amfani da kayansu (ARPU), musamman abin da ya shafi sarrafa murya a harkar kasuwanci, yana tattare da boyayyar nasa na sababbin kafafen sadarwa da ke ci masa dunduniya (OTT), da rashin ingancin ayyukan sadarwar tare da karuwar bashi da dimbin kasha kudi. daukacin wadannan al’amura su suka tattaru suka kawo tarnaki ga masu hada-hada a wannan masana’anta,” inji shi.
Tsawon shekaru a cewarsa, hukumar ta samu dimbin nasarori wajen daidaita al’amura a wannan masana’anta, amma duk da haka ta yi matukar damuwa da rashin garkuwar da za ta bai wa hada-hadar masana’anta da ke da lasisin kasuwanci a daukacin kasuwanni da ke tattare da alfanu.
A cewars, al’amuran da suka faru a masana’antar nan a kwanakin nan da suka wuce sun bijiro da bukatar daukar matakin gaugawa ga masu ruwa da tsaki su aiwatar da dabarun harkokin mulki managarta da aka jarraba su wajen gudanar da harkokin kasuwanci.
Shugaban Hukumar NCC ya ce daga wani yanki na tsare-tsaren hukumar da ke tallafawa wajen bayar da lasisin cimma manufa, za ta fara sa-ido kan harkokin da ke da alaka da dokar.
Ya ce “bisa ka’idar managarciya da aka tsara ta bin Kadin ala’amura don tabbatar da aiwatar da tsarin, ya far aaiki ne daga watanni ukun saahekarar 2017 da suka gabata, inda hukumar za ta kara kaimi wajen sa-ido kan harkokin da ke da dangantaka da dokar. Kuma hukumar za ta rika yin gwsajin gano al’amuran da ke tattare da kawo tarnaki daga lokacbi zuwa lokaci kan lasisin da ta bayar, don tabbatar da ingancinta kan yadda ake tafiyar da al’amura bias tsarin dokokin Najeriya. Mun fahimci hikimar nan da ke cewa “wanda duk ya taba cutuwa to zai yi matukar takatsantsan. Don haka ba za mu so ganinrushewar manyan kamfanonin waya sadarwa, wadanda muka dauka a matsayin mabubbugar bunkasar tattalin arziki a kasar mu.
Shi ma AMtaimakin Shugaban hukumar NCC Farfesa Umar dambatta da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron, cewa ya yi, ko tantam babu masana’antar hada-hadar harkokin sadarwa turakun tallafar dorewar bunkasa tattalin arzikin kasa ne, wanda ci gaban kasa da bunkasarta ya dogara a kai.
“Irin wannan ne ya sanya masana;anta za ta kasance ja-gaba ta hanyoyi da dama da za su tabbatar mana da kwarin gwiwar da ake bukatza don kaiwa wani matsayi da dimbin jari da samar da kudin hada-hada da za su bunkasa tattalin arzikinmu da samar da kyakkyawar makomar ci gaba,” inji Farfesa dambatta.
Ya ce bincike ya gano cbewa ba da dadewa ba a wani binciken da aka yi cikin shekarar 2016 a Singapore (na rahoton jan ragamar harkokin mulki 2016) ya nuna sabanin hakan bisa la’akari da cewa kyakkyawan tsarin jagoranci dai haifar karin hada-hada kudi, inda aka gano cewa a wasu kasashen da ake da kyakkyawan tsarin jan ragamar harkokin mulki a masan’antu ana samun dimbin zuba jari da hada-hadar kudi mai yawa da ke haifar da ragowar kashe kudi na matsakaici zuwa dogon lokaci.
Ya ce bin managarcin tsarin jan ragamar kamfanoni ke haifar da fuskantar samar da alfanum bunkasar tattali mai dorewa.
Ya ce, “Rahoton Bankin Duniya na baya-bayan nan ya bayyana cewa Najeriya ta samu karin maki zuwa 24 a matakin manuniyar duniya kan saukaka harkokin kasuwanci ya nuna cancantar smaun kimar makin. Yunkurin da aka yin a kaitsaye da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi a karkashin tsarin farfado da tattalin arziki (ERGP) wanda ke da manufar hada-hadar zuba jarin kasuwanci gaskiya keke-da-keke, al’amarin da zai jawo hankalin masu zimmar zuba jari su fara aiwatar da tsarin saukaka harkokin kasuwanci bisa tssarin da gwmanatin tarayya ta fitar, karkashin ajgorancin jiga-jigan jan ragamar tsarin Gwmanatin Tarayya na farfadowa da bunkasa tattalin arziki, karkashin Shugabancin Mataimakin Shugaban kasa. kokarin da ake yi a wannan fanni cikin shekara biyu ya haifar da kyakkyawan sakamako. Tasirin wannan kyakkyawan sakamako shi ya samar da masu saka jari daga kasar waje a wannan dan tsakanin lokaci.
“A dai karkashin shirin bunkasa tattalin arziki na ERGP za a kara bunkasa amfani da intanet da sauran kayan fasahar sadarwa, wadanda aka tabbatar da cewa sune jigo wajen karkata akalar bunkasa tattalin arziki fiye da yadda aka dogara kacokam da albarkatun man fetur da iskar gas.
‘Bisa la’akari da kimar fasahar kere-kere da ke tashe wajen hargitsa tattalin arzikin duniya harkokin sadarwa da fasahar sadarwa ssu ne jigo juya akalar cimma daukacin manufofi kamar yadda yake kunsshe a kundin shirin bunkasa tattalin arziki na ERGP. Babu wani sashe na tattalin arziki da ba ta dogara da harkokin sadarwa da fasahar sadarwa. Za a iya ambaton harkar kula da lafiya kyautata zamantakewa da harkokin sufuri, da sarrafa kayan aiki ga wasu masana’antu da noma da kasuwanci da ilimi da nishadi da sauransu.
Ya ce bayan da aka yi sun tabbatar da muhimman al’amura da ke da tasirin cimma manufarmu ta na ci gaban kasa, don haka akwai bukatar ganin wannan fani ya kasance a kan gaba wajen aiwatar da gaskiya keke-da-keke ta’adun da ake bukata don tabbatar da tsare-tsaren doka.
Ya ce don nuna gamsuwa da muhimmancin wannan sashi wajen cimma wadannan manufofi, NCC ta jajirce wajen daidaita managartan ayyuka ta yadda wannan fanni zai zama mai matukar muhimmanci da ke jan ragamar saka hannun jari da hada-hadar kudin da ake bukata.
A cewarsa, rahoton tantance matsayin masana’antar na nuni da cewa mafi yawan kalubalen da ke kawo tarnaki ga wannan fanni suna da alaka da tsare-tsaren gudanarwa marasa kyau.
“’Ba dadadewa ba ne Majalisar Wakilai ta Najeriya a wani taron sauraron kkoken al’umma da ta shirya kan ingancin wannan fani aka gano cewa akwai dimbin haraji na Naira Biliyan 143 da ba a biya gwamnati ba. Idan an cire son rai wannan dimbin kudi na nuni da cewa rtashin biyansu bai rasa nasa da mummunan tsarin gudanarwa. Kyakkyawan tsarin da ke bayyana al’amura a ganinmu ba za su bar dimbin bashi ya taru ba.
Sannan hukumar da ke daidaita al’amura na takun saka da kamfanonin waya kan rajistar layi dda yawan datar da suke samarwa da wakilansu a karkashin dokar rajistar layi, al’amarin da ke tattare da tsaron kasa. Wadannan matsaloli sun bijiro ne sanadiyyar mummunan tsarin tafiyarwa da tanadin doka, al’amuran da wannan taron kara wa juna sani ke kokarin fadakar da mu a kai.
NCC ta ce ta hanyar doka take neeman managarcin tsarin hadin gwiwa, a matsayin jigon hada karfi da amana don karfafa gwiwar masu zuba jari ta hanyar tsare-tsaren bayyana gaskiya keke-da-keke. Cikakken bin ka’ida zai haifar da daidaituwar al’amura a tsakanin masu hada-hada cikin lokaci.
Ya ce dorewar ci gaban da aka samu daidai da kimar managarcin tsarin aiwatar da ayyuka a duniya zai tabbatar da cewa wannan fanni ya tsayu da karfinsa wajen jan ragama ko mai karfafawa, kan irin gudunmuwar da take bayarwa wajen juya akalar tattalin arzikin duniya.
Yadda bunkasar fasahar kere-kere ke kawo tarnaki ga tsarin al’adar tafiyar da tattalin arziki, wannan fanni dole ne ya yi tasirin samar da karfin kariyar da ake bukata don shawo kan kowace irin matsala, ta yadda daukacin rudanin kan kasance kirkirarre ne da ke da kyawun fasali, a cewar Farfesa dambatta.
“Muna karfafa gwiwar bin ka’ida domin babu kamfanin da ya san abin da yake da zai yi ikrarin kin bin managarcin tsarin aiwatar da aiki a fadin duniya. Bisa la’akarin da kudin da za a kashe wajen aiwatar da ka’idojin dokar, sai aaka fito da tsare-tsaren da aka karkasa kamfanoni a wannan fanni kan yadda za su dabbaka doka,” inji shi.
Ya ce duk da yake ba su ne jigon tabbatar da aiwatar da dokar ba, sai dai an sanya takunkumin don tabbatar da bin ka’idar dokar.
‘Akwai lada da karramawa ga wadanda sukakyautata wajen cikakken bin ka’ida da aiwatar da dokar akai, akai,’ inji shi.