Daliba da mahaifiyarta sun kawo ’yan daba su kai hari a makarantarsu
Ana cikin taro suga shigo makarantar da karti, suka tayar da hankalin jama’a
Wata dalibar makarantar sakandare da mahaifiyarta sun kai ’yan daba makarantarsu domin su lakada wa wani dalibi duka.
Bayan faruwar lamarin a garin Ibadan na Jihar Oyo, Kwamishinan Ilimin jihar, Rahman Abiodun Abdu-Raheem, ya ce gwamnatin jihar dakatar da dalibar daga makaranta.
- Daliba ta bude shafin koyar da Lissafi da harshen Hausa
- Mutum na farko ya kamu da kwayar cutar Omicron a Saudiyya
Kwamishinan ya ce, “Mahaifiyar dalibar da sauran kartin ne suka tayar da yamutsin, amma gwamnatin jihar za ta dauki karin matakai da za su zama izina ga iyaye da dalibai da ba su san abin da ya kamata ba.”
Ya bayyana cewa ana tsaka da taron iyaye da malamai ne dalibar, wace take biye da mahaifiyarta suka shigar makarantar da wasu karti, majiya karfi, suna neman dalibin.
A nan ne suka lakada wa dalibin duka, suka kuma ci mutuncin wasu daga cikin malamai da iyayen dalibai da ke halartar taron.
Kwamishinan ya ce bayan dakatar da dalibar, Gwamnatin Jihar Oyo ta dauki matakan hukunta duk masu laifi domin hana samun tashin hankalin ko baraza ga makarantar, malamanta, da dalibai ko iyayensu.