Daliba Mafi Hazaka ta Duniya ta lashe wani sabon kambu
Bayan lashe kambun Daliba Mafi Hazaka ta Duniya, Fareedah ta sake lashe wata kyautar.
Dalibar nan ’yar Najeriya da ta laba lashe kambun Daliba Mafi Hazaka ta Duniya, Fareedah Oyolola, ta sake lashe kambun gasar lissafi.
Fareeda Oyolola ta yi wa sauran daliban da suka fafata a gasar ta lissafi da aka kammala a watan Disamba fintakau, inda ta samu maki 97.2 cikin 100.
- Kisan Hanifa: Kotu ta dage sauraron shari’ar Abdulmalik Tanko
- Daga Laraba: Yadda labaran karya ke hana ruwa gudu a cikin al’umma
“Wannan labari ne mai dadi, Fareedah ’yar baiwa ce kuma ta wakilce mu, iyayenta da kuma makarantar Greensprings, muna alfahari da wannan nasara da ta samu,” a cewar Mataimakiyar Daraktar Ilimin makarantar, Dokta Barney Wilson.
Gasar lissafin an shirya ta ne don ba wa daliban damar zurfafa tunaninsu wajen warware matsala tare da fahimtar yadda batun ya ke.
Cibiyar Johns Hopkins ta karrama Fareedah Oyolola a matsayin daya daga cikin dalibai mafiya hazaka a duniya a watan Disamba, 2021.
Da take bayyana ra’ayinta game da lashe kambun gasar, Fareedah ta ce, “An yi mana gwaji na furuci da kuma lissafi inda na amsa tambayoyi 100 cikin minti 44! A karshen gwajin na samu kaso 92 cikin 100 a furuci, yayin da na samu kaso 87 a lissafi.
“Babu yadda za a yi a ce na ci wannan maki a kankanin lokaci ba tare da taimakon malamaina ba, saboda su ne suka jajirce wajen horar da ni har na samu gogewa a bangaren lissafi, ina matukar gode musu,” inji Fareedah.
A wata sanarwa da Cibiyar Shirya Gasar Dalibai Masu Hazaka ta fitar ta hannun Babban Daraktar cibiyar, Virginia Roach, ta taya Fareedah da sauran gwarazan dalibai a fadin duniya murnar lashe kyaututtuka daban-daban.
Ta ce, “Muna farin cikin taya wadanan daliban murnar nasarar da suka yi. Muna farin cikin kasancewar wadanda za su taimaka musu wajen zama manyan fasihai a rayuwarsu.”
An fara wallafa wannan labarin ne a jaridar Teen Trust ta ranar 1-7 ga watan Fabrairu.