Daliba ta rasu ana tsaka da daukar lacca

Aminat ta rasu ranar jajibirin bikin rantsar da su a matsayin sabbin dalibai, wanda ya zo daidai da zagayowar ranar haihuwarta

Daliba ta rasu ana tsaka da daukar lacca

Wata dalibai ta yanke jiki ta fadi a mace a yayin da suke tsaka da daukar lacca a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara.

Dalibar mai suna Aminat Akanke Tajudeen ta rasu ne a ranar jajibirin bikin rantsar da su a matsayin sabbin daliban kwalejin.

Abokan karatun marigayiyar sun ce ranar Alhamis din da aka tsara bikin rantsar da su din ya zo daidai da zagayowar ranar haihuwar Aminat, amma ta rasu a ranar Laraba.

Aminiya ta gano cewa Aminat ta riga karbo rigarta ta bikin rantsarwar, kafin mutuwarta bayan da ta yanke jiki ta fadi a aji.

Wani jami’in kwalejin ya ce an garzaya da Aminat zuwa asibitin kwalejin, amma ko kafin a isa rai ya riga ya yi halinsa.

Wata daliba mai koyon aikin jinya wadda kuma take cikin wadanda suka duba marigayiyar a asibitin, ta ce duk da cewa a mace aka kawo Aminat, sun tura su zuwa Babban Asibitin Ilorin don guje wa zanga-zangar dalibai.

Daga bisani dai an yi jana’iyar dalibar aka kuma binne ta bisa tsarin addinin Islama a makabartar Musulmi da ke Osere.

Mahaifin Aminat, Akanke ya shaida wa Aminiya cewa babu wata alamar matsala ko rashin lafiya a tare da mariygayiyar a lokacin da suka rabu.

Ya ce sai da suka yi doguwar hira da ita, sannan shi da kansa ya raka ta zuwa inda ta hau tasi ta tafi makaranta.

Jami’ar huld da jama’a ta kwalejin, Misis Abibat Zubair ta bayyana cewa an yi juyayin Aminat a taron rantsar da sabbin daliban kuma shugaban kwalejin da dalibai sun kai wa mahaifan Aminat ziyarar ta’aziyya.