dalibai 12 ke kwance a asibiti saboda shan wani magani a Ebonyi

Akalla daliban makarantar sakandaren Ginger International 12 ne da ke Abakalike, Jihar Ebonyi ke kwance a wasu asibitoci da ke birnin na Abakalike sakamakon shan maganin tsutsar ciki da hukumar makarantar ta ba su.Hukumar Makarantar wadda ke a unguwar Hausawa Abakalike ce ta bayar da maganin tsutsar cikin, kamar yadda Aminiya ta samu labari. Al’amarin […]

dalibai 12 ke kwance a asibiti saboda shan wani magani a Ebonyi
dalibai 12 ke kwance a asibiti saboda shan wani magani a Ebonyi

Akalla daliban makarantar sakandaren Ginger International 12 ne da ke Abakalike, Jihar Ebonyi ke kwance a wasu asibitoci da ke birnin na Abakalike sakamakon shan maganin tsutsar ciki da hukumar makarantar ta ba su.
Hukumar Makarantar wadda ke a unguwar Hausawa Abakalike ce ta bayar da maganin tsutsar cikin, kamar yadda Aminiya ta samu labari. Al’amarin da maimakon gyaran lafiyar daliban da ake tsammani sai ya rikide ya zama jangwam.
Bayanin da wakilinmu ya samu daga asibitin da daliban ke kwance ya nuna cewa wasu mutum biyu na kwance a dakin karbar marasa lafiya na gaugawa a asibitin koyarwa na Gwamnatin Tarayya, yayin da ragowar mutane goma kuma ke can asibitin ’yan sanda, duk a birnin na Abakalike. Binciken da aka gudanar ya gano cewa daliban da abin ya shafa, shekarunsu sun kama daga 12 zuwa 15 ne da haihuwa.
Hajiya Bilkisu Ahmed ta yi zargin cewa: “Wani melami ne ya matsa wa ’yata shan maganin.” Mahaifin wani dalibin mai suna Sam Igwe, shi kuma cewa ya yi: “Ni an bai wa dana ne maganin ya sha ba tare da sanina ba.”
Babban daraktan asibitin, Emeka Onwe ya shaida wa Aminiya cewa: “Mun karbi samfurin kwayoyin, mun aika wa hukumar kula da ingancin abinci da kuma magunguna (NAFDAC), domin su yi mana bincike; da zarar sun kammala suka ba mu sakamako, za mu zo da bayani.” Inji shi.