dalibai 12 sun yi saukar Alkur’ani a Madarasatu Nuril kur’an ta Dungurawa

A ranar Asabar ne aka yi bikin saukar karatun dalibai 12 a Makarantar Islamiyya ta Madarasatu Nuril kur’an da ke Dungurawa a karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano. Shugaban Makarantar Malam Abubakar Shu’aib Gwamai, ya shaida wa Aminiya jim kadan da kammala saukar karatun cewa, an kafa makarantar ce a shekarar 2007 da dalibai […]

dalibai 12 sun yi saukar Alkur’ani a Madarasatu Nuril kur’an ta Dungurawa
dalibai 12 sun yi saukar Alkur’ani a Madarasatu Nuril kur’an ta Dungurawa

A ranar Asabar ne aka yi bikin saukar karatun dalibai 12 a Makarantar Islamiyya ta Madarasatu Nuril kur’an da ke Dungurawa a karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano.

Shugaban Makarantar Malam Abubakar Shu’aib Gwamai, ya shaida wa Aminiya jim kadan da kammala saukar karatun cewa, an kafa makarantar ce a shekarar 2007 da dalibai 25 da malamai uku, amma yanzu makarantar tana da dalibai fiye da 400 da malamai da dama.
Dukkan dalibai 12 da suka sauke Alkur’ani a wannan rana sun halarci wajen bikin tare da ’yan uwa da abokan arziki domin shaida wannan rana mai dimbin tarihi, kuma wakilan karamar hukuma da na Hakimin Dawakin Tofa sun kasance a wurin kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.
Tunda farko a jawabinsa wajen saukar karatun, Malam Abubakar Gwamai ya ce sun fuskanci kalubale iri-iri wajen kokarin kafa makarantar, ciki har da tabbatar da zuwan yara makaranta a kan lokaci da kuma samar da kayan karatu.
Sai ya yaba wa malamai da iyayen yara saboda jajircewar da suke yi har Allah Ya sanya makarantar ta kasance daya daga cikin makarantu da ake alfahari da su a yankin, inda ya yi amfani da wannan biki wajen isar da godiyar hukumar makarantar ga wakilin Hakimin Dawakin Tofa kuma danmalikin Dawakin Tofa, Alhaji Aminu Sulaiman Dungurawa da wakilin karamar hukumar, kuma mai bai wa shugaban karamar hukumar shawara ta musamman Alhaji Nuhu Halilu Gwamai bisa tallafa wa ilimi da suke yi ba tare da gajiyawa ba.
Ya ce da yardar Allah makarantar za ta ci gaba da samar da dalibai masu nagarta ta yadda al’umma za su kara amfana da kafuwarta.