dalibai 200 sun yi sauka a Madarasatul Darul Huda da ke Gombe
Makarantar Madarasatu Darul Huda da ke gidan marigayi Malam Muhammadu Basakkwace a Unguwar Tudun Wadan Gombe ta yaye dalibai 200 da suka sauke Alkur’ani Mai girma a karo na shida. Da yake jawabi a lokacin saukar karatun Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, kira ya yi ga daliban da suka yi saukar cewa akwai kalubale […]
Makarantar Madarasatu Darul Huda da ke gidan marigayi Malam Muhammadu Basakkwace a Unguwar Tudun Wadan Gombe ta yaye dalibai 200 da suka sauke Alkur’ani Mai girma a karo na shida.
Da yake jawabi a lokacin saukar karatun Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, kira ya yi ga daliban da suka yi saukar cewa akwai kalubale a gabansu na ci gaba da nazarin littatafan ilimi.
Gwamna dankwambo, wanda ya samu wakilcin Uban Doman Malala Alhaji Usman Manu Malala, ya ce a lokacin da suke neman ilimin littattafai su hada da ilimin zamani domin su samu na zaman duniya.
Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, wanda tsohon Alkalin Alkalan Jihar Alhaji Usman Baba Liman ya wakilce shi, cewa ya yi Malam Muhammadu Basakkwace, ya rasu ya bar sadaka mai gudana domin wannan makaranta tasa tana daga cikin irin abin da ake son mutum ya gina kafin ta Allah ta same shi.
Sarkin ya yi kira ga iyayen yara da hukumomin gwamnati da masu hannu da shuni su rika taimaka wa irin wadannan makarantu kasancewar akwai bukatu kuma kyauta ake karatu ko kudin mako-mako ba a karba balle na wata-wata daga dalibai.
Shugaban taron tsohon Kwami-shinan Ilimi na Jihar Dokta Habu dahiru, ya ce babu yadda za a yi a samu al’umma kimtsattsiya sai da ilimi.
Dokta Habu Dahiru, ya yi kira ga al’umma su yi koyi da marigayi Malam Muhammadu Basakkwace, wajen gina makarantun Islamiyya don ilimantarwa da tarbiyyantar da jama’a.
Ya bada shawarar a yi wa makarantar rijista da hukumar ilimi don ba dalibanta damar samun takardun shaidar da za su iya tafiya jami’o’in Musulunci ko wasu jami’o’i na gwamnati.
Da yake ba da takaitaccen tarihin makarantar Malam Garba Tudun Wada, ya ce an gina makarantar ce shekara 45 da suka gabata kuma da shi aka fara amma yanzu makarantar tana da rassa 49 a sassan Gombe.
Malam Garba Tudun Wada, ya ce dalibai 12 suka fara yin sauka a makarantar a shekarar 2003, yanzu a karo na shida dalibai 200 maza da mata suka sauke, yayin makarantar take da dalibai dubu 3,353 da malamai 71.