dalibai 224 suke fafatawa a gasar Musabaka ta Jigawa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira miliyan 29 domin gudanar da Musabakar Karatun Alkur’ani ta bana, wadda aka fara a garin Dutse fadar jihar. Shugaban shirya gasar Musabakar ta Jihar kuma Babban Sakataren Hukumar Harkokin Addini ta Jihar Alhaji Yakubu Abbas Yakubu ya sanar da manema labarai haka a ganawa da su lokacin bude Musabakar […]
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira miliyan 29 domin gudanar da Musabakar Karatun Alkur’ani ta bana, wadda aka fara a garin Dutse fadar jihar.
Shugaban shirya gasar Musabakar ta Jihar kuma Babban Sakataren Hukumar Harkokin Addini ta Jihar Alhaji Yakubu Abbas Yakubu ya sanar da manema labarai haka a ganawa da su lokacin bude Musabakar a ranar Litinin.
Alhaji Yakubu Abbas ya ce an zabo dalibai 12 daga kowacce karamar hukuma daga cikin kananan hukumomin jihar 27, maza 6 da mata 6 da zasu wakilci kananan hukumomin inda daga nan ne za a samu zakarun da za su wakilci jihar a gasar kasa da za a yi nan gaba.
Ya ce dalibai 224 aka zabo daga kananan hukumomin wadanda an riga an tantance su kuma gaba dayansu ’yan asalin jihar ne kamar yadda gwamnati ta nema, saboda za a dauki nauyin karatunsu zuwa kasashen waje.
Ya ce duk shekara gwamnatin jihar tana daukar nauyin dalibai masu zuwa karatun addini zuwa kasar Sudan da Saudiyya da Masar.