Dalibai 30,000 sun yi nasarar rancen kudin karatu a kwana 6

Manajan Daraktan asusun bada rancen kudin karatu na Najeriya (NELFUND), Mista Akintunde Sawyerr, ya ce sama da dalibai 60,000 ne suka mika bukatar neman rancen kudin karatu tun bayan bude shifin NELFUND ga daliban manyan makarantu a ranar Juma’ar da ta gabata. Sawyerr, ya bayyana cewa daga cikin 60,000 da suka cike takardun nema rancen, […]

Dalibai 30,000 sun yi nasarar rancen kudin karatu a kwana 6

Manajan Daraktan asusun bada rancen kudin karatu na Najeriya (NELFUND), Mista Akintunde Sawyerr, ya ce sama da dalibai 60,000 ne suka mika bukatar neman rancen kudin karatu tun bayan bude shifin NELFUND ga daliban manyan makarantu a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sawyerr, ya bayyana cewa daga cikin 60,000 da suka cike takardun nema rancen, 30,000 sun yi nasara.

Yayin wata zantawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Manajan Daraktan ya ce “Tururuwar da daliban su ka yi wurin gaggawar cike takardun wata babbar alama ce da ke bayyana buƙatar neman agajin a tsakanin ɗaliban Najeriya.

“Muna farin cikin sanar da jama’a cewa, sama da kashi 90% na jami’o’in tarayyar Najeriya sun mika bayanan dalibansu ga NELFUND.

“Muna kira ga sauran jami’o’i guda biyu da kuma kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya guda biyar da suka rage da su hanzarta  kammala aikin domin tabbatar da cewa duk daliban da suka cancanta sun samu rancen.”

Manajan-daraktan ya ce asusun zai bude shafin ga daliban manyan makarantun jihohi ranar 25 ga watan Yuni, 2024.