dalibai a Amurka sun soki lamirin sayen teburin taro na Naira miliyan 37

daliban jami’ar New Jersey a kasar Amurka, sun soki lamirin jami’an hukumar makarantarsu, wajen sayen teburin taro kan kudi Dala dubu 219, wato daidai da Naira miliyan 36,792,000.Wasu daga cikin daliban jami’ar New Jersey Kean sun koka kan yadda hukumar jami’ar ta sayi teburin shirya taro mai fadin kafa 22, tare da na’urori sarrafa sauti […]

dalibai a Amurka sun soki lamirin sayen teburin taro na Naira miliyan 37
dalibai a Amurka sun soki lamirin sayen teburin taro na Naira miliyan 37

daliban jami’ar New Jersey a kasar Amurka, sun soki lamirin jami’an hukumar makarantarsu, wajen sayen teburin taro kan kudi Dala dubu 219, wato daidai da Naira miliyan 36,792,000.
Wasu daga cikin daliban jami’ar New Jersey Kean sun koka kan yadda hukumar jami’ar ta sayi teburin shirya taro mai fadin kafa 22, tare da na’urori sarrafa sauti da sauran na’urorin lantarki da ke like a jikinsa, wadanda ke amfani da fasahar sadarwa a sassa 25 na duniya.
“Wannan abin takaici ne,” a cewar sabon dalibi Melrose Johnson. “Wannan teburi ne kawai. Zama kawai za ka yi a kansa,” inji shi.
Teburin mai kujeru 23, wani kamfani ne ya kera shi a kasar Sin, domin jami’ar ta bude reshenta. Sai dai jami’an hukumar jami’ar sun ce, za a iyabayar dakin da aka ajiye teburin haya,ta yadda za a rage yawan kudin da aka kashe wajen samar da teburin.
Wasu daliban kuwa, sun shiga shafin sadarwa na twitter, inda suka bayyana cewa, kamata ya yi a kashe kudin wajen kula da al’amuran da suka shafi dalibai, kamar samar da teburan aji da dakin abinci da wurin ajiye ababen hawa ko rage kudin makaranta.