Dalibai a Indiya sun yi zanga-zanga saboda an tozarta wata daliba

Daliban wata kwaleji a Jihar Kerala da ke Kudancin kasar Indiya, sun gudanar da zanga-zanga, bayan wani malami a makarantar ya danganta nonota wata daliba da kankana. An watsa hoton bidiyon da aka dauka lokacin da malamin ke fada wa dalibar wannan kalma a kafafen sada zumunta a karshen makon jiya, lamarin da ya janyo […]

Dalibai a Indiya sun yi zanga-zanga saboda an tozarta wata daliba

Daliban wata kwaleji a Jihar Kerala da ke Kudancin kasar Indiya, sun gudanar da zanga-zanga, bayan wani malami a makarantar ya danganta nonota wata daliba da kankana.

An watsa hoton bidiyon da aka dauka lokacin da malamin ke fada wa dalibar wannan kalma a kafafen sada zumunta a karshen makon jiya, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce, inda mutane ke ta mayar da martani a fusace, musamman mata.

Hoton bidiyon da aka sanya a kafafen sada zumuntar, shi ya harzuka wadansu dalibai inda suka bi tituna, hannuwansu rike da kankanar da aka yayyanka suna zanga-zangar kin amincewa da irin wadannan kalamai ga mata kamar yadda BBC ta ruwaito.

Malamin dai Farfesa ne da ke koyarwa a Kwalejin Farook da ke Kerala, ya kuma fada wa dalibar kalmar ce saboda yanayin shigar da ta yi inda ta bar kirjinta a waje, da kuma wasu sassan jikinta.

Wannan shiga da dalibar ta yi ne ya fusata Farfesan, saboda ya ga kamar ba ta yi shigar mutunci ba, shi ya sa ya ce mata, nononta kamar kankana.

Wata kungiyar kare hakkin matasa a jihar, ta ce ba za ta lamunci cin zarafin mata ta hanyar fada musu duk maganar da aka ga dama ba.

Duk wani yunkuri da manema labarai suka yi domin jin ta bakin Hukumar Gudanarwar Kwalejin ko malamin a kan wannan batu, ya ci tura.