dalibai da kungiyoyin sa-kai sun yi zanga-zanga kan tabarbarewar ilmi

daruruwan jama’a daga kungiyoyin sa-kai hade  da  dalibai   sun  gudanar da zanga-zangar  lumana  a Ikko  kan  abin da   suka  kira  rikon  sakainar  kashi  da  masu  rike da  madafan  iko  na  Najerira  ke yi wa harkokin ilimi, musammam  ma da yake  yanzu  malaman jami’a  suna  yajin aiki kuma gwamnatin tarayya  ta yi biris da al’amarin.Masu zanga-zangar,  […]

dalibai da kungiyoyin sa-kai sun yi zanga-zanga kan tabarbarewar ilmi

Wani yanki daga cikin jama’ar da ta gudanar da zanga-zanga a Legas ranar Talatadaruruwan jama’a daga kungiyoyin sa-kai hade  da  dalibai   sun  gudanar da zanga-zangar  lumana  a Ikko  kan  abin da   suka  kira  rikon  sakainar  kashi  da  masu  rike da  madafan  iko  na  Najerira  ke yi wa harkokin ilimi, musammam  ma da yake  yanzu  malaman jami’a  suna  yajin aiki kuma gwamnatin tarayya  ta yi biris da al’amarin.
Masu zanga-zangar,  wadanda  suka  kwashe  sama  da kilomita   20  suna  tafiya da  kafa  suna  kalaman sukar gwamnati dauke da kwalaye da ke  da rubuce-rubuce kan haka, sun ce sun dinka  wannan  zanga-zangar ke nan har sai ranar da gwamnatin tarayya  ta  sake matsayi  game da ilimi kuma ta saurare su.
Masu zanga-zangar dai sun tashi  daga ofishin kungiyar  kwadago ne  zuwa  ofishin gwamna,  inda suka mika takardarsu wadda  suka bukaci a mika wa  Shugaba Jonathan. Gwamnatin Jihar  Legas ta karbi wasikar  tare  da alkawarin za ta mika wa Shugaba  Jonathan ba da jimawa ba.
Bayan sun bar  ofishin gwamna  ne kuma suka zarce  dandalin marigayi Cif Gani Fawehinmi inda mutane daban-daban suka yi jawabin sosa rai game da  harkokin ilimi a Najeriya, lamarin da ke hana ci gaba, kuma ana iya gyarawa kodayake an baro shiri can baya.
Kwamared Abiodun Aremu  na kungiyar  kare  hakkin bil’adama  ya ce  abin da ya sa  da  yawancin mahukuntan  kasar  ke  nuna halin ko-oho  ga harkokin ilimi  shi ne  saboda ’ya’yansu ba sa karatu a cikin gida Najeriya, idan ma suna yi, sai ka taras makarantar kudi suke  zuwa,  don haka idan makarantun gwamnati  sun  sukurkuce  ba abin da ya dame su.
Shi ma  shugaban  dalibai  na  jihohin Kuda maso Yamma, Kwamared Salami  cewa  ya yi  ilimi  da ya dace  a ce yana sahun gaba  wajen samun fifiko  a kasafin kudin kasa,  yau ya zame baya ga dangi. “Babban abin bakin cikin shi ne  yadda  gwamnati ke aiwatar  da  harkokin ilimi  a  takarda  maimakon a  aikace  ya ce  tun  kafin  malaman jami’a  su fara yajin aikin sai da  suka sanar da  gwamnatin tarayya, amma sai ta yi biris da su kuma da suka fara, sun kwashe  makonni,  ba  wanda  ya ce  musu uffan, sai surutai  gwamnati ke yi ta  kafofin  yada labarai”. Inji shi.