dalibai na ci gaba da karatu a kasa a makarantun Jigawa
Duk da makudan kudin da gwamnatin Jihar Jigawa take kwarmato ta kashe a kan inganta harkokin karatu da gyaran makaramtu da kuma sukar tsohuwar gwamnatin Alhaji Sule Lamido cewa ta bar makarantun jihar ba kayan zama da rubabbun ajujuwa, yau shekara daya da amsar ragamar mulkin jihar har yanzu dalibai ba su da wadatattun kujeru […]

Duk da makudan kudin da gwamnatin Jihar Jigawa take kwarmato ta kashe a kan inganta harkokin karatu da gyaran makaramtu da kuma sukar tsohuwar gwamnatin Alhaji Sule Lamido cewa ta bar makarantun jihar ba kayan zama da rubabbun ajujuwa, yau shekara daya da amsar ragamar mulkin jihar har yanzu dalibai ba su da wadatattun kujeru a makarantun inda dubban dalibai suke ci gaba da daukar darasi a kasa.
Wakilinmu wanda ya zagaya kofar Arewa da Dubantu da Matsaro da ke Hadeja da kuma makarantar Batali da ke gari babura inda Gwamna Muhammad Abubakar Badaru ya fito ya iske ba wani gyaran a zo a gani aka yi makarantu ba, inda shugabannin makarantun suke kokawa game da rashin ingancin gine-ginen da kayan da aka sa a gine-ginen musamman kofofi da kujerun da ’yan kwangila suka kai, suna zargin kamar an yi kashe-mu-raba ne da ’yan kwangila da wasu jami’an Hukumar Ilimi Bai-daya ta jihar (SUBEB).
A makarantar kofar Arewa, wakilimnmu ya samu korafin cewa kofofin da aka sanya musu ba su da inganci kuma kujerun da aka kai marasa inganci ne.
Da wakilinmu ya tuntbi shugaban makarantar Malam Mohammed B. ya roki tsofaffin daliban makarantar da ke da mukami a gwamnatin jihar da ta tarayya da wadanda ke yin aiki a sauran hukumomi da cibiyoyi su taimaka wajen gine makarantar tare da samar mata da tsaro, inda ya ce ’yan daba da mashaya suna shaye-shaye a harabar makarantar tare da mayar da ita hanya suna kade dalibai da abubuwan hawa a lokacin karatu.
Shi ma shugaban makarantar firamare ta Batali Malam Rabi’u Nuhu cewa ya yi makarantar tana fama da karancin malamai da rashin katanga da karancin ajujuwa duk da gyaran da aka yi mata. Kuma ya koka game da karancin kujeru a makarantar, inda ya ce a kasa dalibai suke daukar darasi.
Dayake karin haske a kan lamarin Sakataren Ilimi na karamar Hukumar babura Malam dan’azumi Jazuli ya ce bukaci Hukumar SUBEB ta mike tsaye wajen gyara makarantu domin makarantun jihar a lalace suke, babu inda ake da wadatattun kayan zaman dalibai.
Ya kuma ja kunnen dalibai su rika zuwa makaranta, malamai kuma su guji zuwa aiki a makare, kuma su tsaya a kan aikinsu su ji tsoron Allah domin kauce wa cin haram.
Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Jigawa Malam Salisu Zakar ya nuna damuwa kan halayyar wadansu ’yan kwangila da suke yin aiki ko samar da kayan karatu marasa inganci sabanin yadda aka yi alkawari da su.
Alhaji Zakar wanda ke magana ta bakin Daraktan Mulki na Hukumar Alhaji Suleiman Marke, ya ce gwamnatin jihar ta kashe Naira miliyan bakwai da dubu 400n wajen gyaran makarantar firamare ta kauyen Batali kuma ta kashe Naira miliyan shida da dubu 300 a gyaran makarantar kofar Arewa yayin da ta rushe makarantar firamare ta Dubantu take gina sabuwa mai beni mai dauke da ajujuwa 10 a kan Naira miliyan 32 da dubu 23.
Ya ce gwamnatin ta ware biliyoyin Naira domin sayo kujerun zama a daukacin makarantun jihar 4,000 domin magance karancin kujeru da ke addabar makarantun firamare da kananan makarantun sakandare da ke jihar.