dalibai sun gurfana a kotu kan zargin boye budurwa
Wasu dalibai biyu sun gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge Waje bisa zarginsu da laifin boye wata budurwa mai shekara 15 (an sakaya sunanta) da ke Unguwar Hotoro Tsamiyar Boka a birnin Kano inda aka yin zargin sun rika lalata da ita. dan sanda mai gabatar da kara Shehu Adamu ya bayyana wa […]
Wasu dalibai biyu sun gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge Waje bisa zarginsu da laifin boye wata budurwa mai shekara 15 (an sakaya sunanta) da ke Unguwar Hotoro Tsamiyar Boka a birnin Kano inda aka yin zargin sun rika lalata da ita.
dan sanda mai gabatar da kara Shehu Adamu ya bayyana wa kotu cewa kimanin mako biyu iyayen budurwar suke nemanta, sai ranar Asabar da ta gabata samarin suka dawo da ita gida tare da bayyana cewa suna tare da ita a tsawon wannan lokaci, lamarin da ya sa mahifiyarta ta kai kara ga ’yan sanda washegari Lahadi.
Ya ce mahaifiyar mai suna Rabi’a Adamu ta shaida wa ’yan sanda cewa bayan boye mata ’ya, daliban sun rika lalata da ita a wannan lokaci.
Lokacin da aka karanta musu laifin da ake zarginsu, daya daga cikin daliban mai suna Mas’ud Adamu mai shekara 30 ya ce, ya yi lalata da yarinyar, yayin da abokinsa Auwalu Inusa mai shekara 27 ya musanta laifin lalata da ita sai dai ya amsa cewa an boye ta ne a dakinsa.
Sai dai budurwar ta ce dukkan samarin sun yi lalata da ita a tsawon lokacin da suka boye ta.
Alkalin kotun Mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya ya dage shari’ar zuwa ranar 2 ga Disamba don ba ’yan sanda damar ci gaba da bincike.
A wani labarin Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wani tsoho mai shekara 70 mai suna Abubakar Mu’azu da ke zaune a Zangon Dakata a karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano bisa zarginsa da laifin yi wa wata yarinya mai shekara takwas fyade.
A tattaunawa da Aminiya, tsohon wanda dan asalin garin Kazaure ne a Jihar Jigawa ya ce makwabtansa ne suka yi masa sharri saboda ba sa ga maciji da shi.
Sai dai ya ce, “‘Ina ganin duniya ta zo karshe a wurina. Ina bukatar addu’a domin na daina wannan abu. Idan har aka sake ni zan koma garinmu inda zan mutu a can.”
Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisba bangaren ayyuka na musamman, Barista Nabahani Usman ya ce Allah ne ya tserar da wanda ake zargin domin matasan unguwar sun so su dauki doka a hannunsu har sun fara dukansa, manya suka shiga tsakani.
Ya ce, “Ba wannan ne karo na farko da ake kawo tsohon ba kan irin wannan zargi. Amman bincikenmu ya gano cewa bai kai ga lalata yarinyar ba, domin likitocinmu sun auna yarinyar sun ga bai kai ga lalata da ita ba. Kuma za mu gurfanar da shi gaban kotu.”