dalibai sun kaurace wa ajujuwa a Jihar Borno
dalibai a Jihar Borno inda kungiyar Boko Haram ke da sansani sun kaurace wa daukar darussa a shekaranjiya Laraba a matsayin nuna alhini kan sace ’yan matan makarantar sakandaren Chibok.daliban da matasa su yi amfani da ranar wajen yin addu’o’i, domin gano inda ’yan matan sama da 200 da ’yan Boko Haram suka sace suke.Sun […]
dalibai a Jihar Borno inda kungiyar Boko Haram ke da sansani sun kaurace wa daukar darussa a shekaranjiya Laraba a matsayin nuna alhini kan sace ’yan matan makarantar sakandaren Chibok.
daliban da matasa su yi amfani da ranar wajen yin addu’o’i, domin gano inda ’yan matan sama da 200 da ’yan Boko Haram suka sace suke.
Sun kuma yi kira ga dalibai a fadin duniya su bi sahunsu wajen kauracewa ajujuwa a jiya Alhamis, domin sanya shugabannin duniya su matsa lamba ga Najeriya ta dauki matakan da suka dace domin ceto ’yan matan.
kaurace wa ajujuwan ta biyo bayan umarnin da shugabannin kungiyoyin malamai da na daliban makarantun Jihar Borno suka yi ne na ware ranar domin nuna jimami da bakin dangane da ci gaba da yin garkuwa da dalibai matan sama da 200, wanda ’yan bindiga suka yi, sama da mako uku da suka gabata, domin ci gaba da matsa wa gwamnati lamba ta kara kaimi don kubutar da ’yan matan.
A jawaban da suka gabatar a taron manema labarai a Maiduguri, daliban sun yi ta rera wakoki rike da kwalaye masu cewa “A sako mana ’yan matanmu.”
Shugaban kungiyar dalibai ta Jihar Borno Kwamared Yusuf Tom, ya idan bayan kwana 40 ba a sako su ba to za su kira gangamin daliban makarantun kasar nan da na wasu kasashen waje domin yin zaman dirshan a filin sukuwa na Maiduguri har sai an sako su, ko kuma su yi tattaki zuwa Chibok tare da kutsawa dajin Sambisa don nemo su.
Shugaban kungiyar Malamai ta Jihar Kwamared Bulama Abiso, ya ce sun lura gwamnati tana rikon sakainar kashi kan lamarin, ganin mako uku ke nan ba ta fito fili ta nuna alhini a kai ba, kuma ba a san halin da suke ciki ba.