dalibai za su rika hutun sallah a Amurka -Magajin Garin New York
Za a fara bai wa daliban makarantun Gwamnati hutun babbar sallah da karama, a Amurka, al’amarin da shugabannin Musulmi da ke birnin New York suka nuna farin da shi, kamar yadda Kamfnain Dillancin LAbarai na AP ya ruwaito. A karkashin sabon tsarin, wannan birni mai ’yan makaranta Musulmi mutum miliya daya da dubu 100, zai […]
Za a fara bai wa daliban makarantun Gwamnati hutun babbar sallah da karama, a Amurka, al’amarin da shugabannin Musulmi da ke birnin New York suka nuna farin da shi, kamar yadda Kamfnain Dillancin LAbarai na AP ya ruwaito.
A karkashin sabon tsarin, wannan birni mai ’yan makaranta Musulmi mutum miliya daya da dubu 100, zai yi hutun sallar layya, wato Eid al-Adha a ranar 24 ga Satumbar bana, sannan a karshen watan Ramadan na badi za a yi hutun karamar salla, wato Eid al-Fitr.
“Dubban daruruwan iyalai Musulmi sun samu waraka daga matsalar zabi tsakanin zuwa makaranta a wadannan ranaku masu albarka,” a cewar Magajin garin birnin, Bill de Blasio, a lokacin da yake bayar da sanarwa.
Su kuma shugabannin Musulmi sun nuna matukar farin cikinsu da wannan sanarwa. “Bayan da aka shafe shekaru al’ummar Musulmin birnin New York na ta fafutikar ganin an rika bai wa Musulmi hutu a wadannan ranaku, yanzu suna cike da farin ciki, ganin cewa ba za a hukunta su ba, saboda yin hutu a ranakun addininsu,” a cewar Zead Ramadan, wani jami’i a majalisar kyautata huldar Musulmi da sauran Amurkawa.
Ita ma Linda Sarsour, wata mai fafutikar ganin an rika bai wa Musulmi hutun sallah a makarantun gwamnati, ta raka Magajin gari Blasio wajen bayar da wannan sanarwar a garin Brooklyn, inda ta ce: “Wannan shi ne manufar birnin New York, wato amincewa da kowa ba tare da la’akari da wnai bambanci ba.”
Toshon Magajin gari Michael Bloomberg ya yi adawa da wannan sauyi da aka samu, amma de Blasio da sauran mafi yawan ’yan takarar da suka fafata da Bloomberg a shekarar 2013, sun amince da aiwatar da sabon tsarin.
Tuni dai Hukumomi a birnin New York suka amince da hutun mabiya addinan Yahudanci na Rosh Hashama da Yom Kippur, tare da na mabiya addinin Kirista, da suka hada da Kirsimeti da Good Friday.
Sauran garuruwan da suka amince da wannan hutu a Amurka, sun hada da Waterbury da Connecticut sa Frederick County da Maryland.