Daliban Chibok 21 sun dawo gida da ’ya’yan Boko Haram 34 —Rahoto

Damuwar sace daliban Chibok ta yi ajalin 48 daga cikin iyayensu kuma har yanzu akwai ragowar 91 daga cikinsu a hannun mayakan kungiyar

Daliban Chibok 21 sun dawo gida da ’ya’yan Boko Haram 34 —Rahoto

Wani rahoto ya nuna cewa 21 daga cikin Daliban Makarantar Chibok da Boko Haram ta sako sun dawo ne da yara 34 da suka haifa wa mayakan kungiyar. 

Rahoton da gidauniyar Murtala Muhammed Foundation (MMF) ta fitar ya ce yawan ’ya’yan da daliban da suka kubuta daga hannun mayaƙan Boko Haram ya tabbatar da tsananin cin zarafi da auren dole da aka yi wa ’yan matan a hannun kungiyar.

Rahoton da gidauniyar ta fitar a karshen mako ya kara da cewa har yanzu akwai 91 daga cikin daliban da ke hannun mayakan kungiyar.

Ya kara da cewa 48 daga cikin iyayen daliban aka sace ne suka mutu tun lokacin da aka sace ’yan matan, wadanda suka rage kuma suna fama da tsananin damuwa da matsalolin lafiya da kuma cikas ga aiki da ilimi.

A watan Afrilu 2014 ne mayakan Boko Haram suka kutsa makarantar kwanan ta dalibai mata suka yi awon gaba da dalibai 276 gab da zana jarabawar kammala sakandare.

A yayin gabatar da rahoton ta zahiri, babbar jami’ar MMF, Dakta Aisha Muhammed-Oyebode, ta bayyana cewa gidauniyar ta fitar da wasu muhimman shawarwari 10 da suka bukaci gwamnatin Najeriya da kasashen duniya su hada kai wajen kai kawo dauki da kuma bayar da hadin kai.

“Bayan abubuwan da aka ba da fifiko sun haɗa da ingantattun matakan tsaro; shirye-shiryen karfafawa al’umma; shirye-shiryen ilimi; gyare-gyaren doka; sadarwa ta gaskiya; taimakon jin kai da taimakon raya kasa; shirye-shiryen ƙarfafa mata da tsarin gargaɗin farko don barazanar tsaro.”

“Muna kira ga hukumomin Najeriya da kasashen duniya da su dauki kwararan matakai don magance matsalolin da ke haddasa rikice-rikice, tsattsauran ra’ayi da cin zarafin mata da ’yan mata, wadanda suka hada da talauci, rashin zaman lafiya da rashin zaman lafiya. damar tattalin arziki.

“Rahoton MMF ya ba da shawarwari a kokarin magance tushen satar mutane tare da yin kira ga hadin gwiwar kasa da kasa da su dauki matakin gaggawa don samar da hanyoyin da za su kawo karshen rikicin.”

Ta kuma ba da shawarar cewa dole ne a tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda ke da hannu a wannan aika-aika a gaban kuliya komi karfinsu ko alakarsu.