daliban firamare na ci gaba da daukar darasi a gindin itatuwa a Dutse

Duk da irin makudan kudi da gwamnatin Jihar Jigawa ke kashewa a fannin makarantun firamare ga alama har yanzu ba ta sake zane ba domin kuwa har yanzu wasu makarantun da suke kwaryar Dutse fadar jihar dalibai na ci gaba da daukar darasi a gindin itatuwa.Makarantun da wakillimu ya ziyarta kuma ya tarar dalibai na […]

daliban firamare na ci gaba da daukar darasi a gindin itatuwa a Dutse

Duk da irin makudan kudi da gwamnatin Jihar Jigawa ke kashewa a fannin makarantun firamare ga alama har yanzu ba ta sake zane ba domin kuwa har yanzu wasu makarantun da suke kwaryar Dutse fadar jihar dalibai na ci gaba da daukar darasi a gindin itatuwa.
Makarantun da wakillimu ya ziyarta kuma ya tarar dalibai na daukar darasi a gindin itatuwa sun hada da firamaren Zobiya inda ya tarar da ajujuwa hudu na ’yan aji daya zuwa uku na daukar darasi a gindin bishiya.
Haka a makarantar firamare ta Gadarawa da ke cikin garin Sakwaya ya ga wani aji da yara ke karatu a gindin itaciya. Kuma an shaida masa cewa malaman makarantar ne suka harhada kudi suka sayi kwano suka katange wani sashi suna bahaya a ciki su da daliban, saboda hukuma ta gaza gina musu.
Da wakilinmu ya tuntubi Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Alhaji Abdullahi Hudu Balangu ya ce ba su ne ke da alhakin lura da makarantun firamare ba, Hukumar SUBEB ce, amma za su yi bakin kokarinsu wajen tuntubar hukumar da duk hukumar da ke da ruwa da tsaki don shawo kan matsalar.
Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Jigawa Alhaji Sani Abdullahi Gumel ya ce shi kansa a wata ziyarar ba-zata da ya kai, ya gane wa idonsa wani aji da aka bari a wulakance a karamar Hukumar Kiyawa, kuma ya lura akwai karancin ajujuwa a makarantar Jigawar Tsada da ke Dutse. Ya ce idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai, don haka hukumar za ta ci gaba da kokarin samar da karin ajujuwa a makarantun firamaren jihar.