Daliban FUT Minna sun kulle VC a waje kan matsalar fashi da makami
Tun da misalin karf 8 na safiyar masu zanga-zangar suka yi kukan kura suka rufe babbar kofar, tun kafin isowar Shugaban Jami’ar
Daliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT) da ke Minna sun gudanar da zanga-zanga kan yawaitar matsalar fashi da makami da ke lakume rayukan abokan karantunsu makarantar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa halin da ake ciki, masu zanga-zangar sun rufe babbar kofar shiga jami’ar, matakin da ya kawo tsaiko ga harkokin karatu a jami’ar.
Tun da misalin karf 8 na safiyar daliban suka yi kukan kura suka rufe babbar kofar, tun kafin isowar Shugaban Jami’ar harabar makarantar.
Koƙarin da Shugaban Jami’ar na lallashin daliban bai yi nasara ba, inda suka nemi ya tafi ya ba su wuri. Sai bayan sa’o’i da dama jami’an tsaron jami’ar suka sama masa hanya ya shiga harabar jami’ar.
Ma’aikata da dama da manyan jami’an gudanarwa da malamai sun kasa shiga cikin jami’ar, inda da yawa daga cikinsu suka koma gida bayan daliban sun nace cewa ba za a sake bari kowa ya shiga ba.
Wannan bore ya gudana ne a yayin da jami’ar ta shirya gudanar da jarabawar kwamfuta ta zangon farko ga daliban mataki na100 zuwa 300, amma shirin ya rushe sakamakon zanga-zangar.
Wani ɗalibi da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa ɗalibi ɗaya ya rasa ransa a wani harin fashi da ya faru kwanaki uku da suka gabata, yayin da wani sabon harin fashi da ya auku daren ranar Talata ya raunata ga wasu daliban.
Wakilinmu ya aiko da hotunan yadda ababen bawa da ma dalibai da suka zo domin daukar darussa suka yi curko-curko a babbar kofar shiga jami’aar a safiyar Talatar nan.