Daliban Isah Gausu sun nemi Hukumar SSS ta saki malaminsu
dalibai da iyalai da ’yan uwan malamin addinin Musuluncin nan na Bidda a Jihar Neja da ake kira Malam Isah Muhammad Awwal da aka fi sani da Malam Isah Gausu sun zargi masarautar Bidda da hannu wajen yin amfani da jami’an Hukumar Tsaro ta kasa (SSS) a kama malamin nasu a bara, inda suka bukaci […]

dalibai da iyalai da ’yan uwan malamin addinin Musuluncin nan na Bidda a Jihar Neja da ake kira Malam Isah Muhammad Awwal da aka fi sani da Malam Isah Gausu sun zargi masarautar Bidda da hannu wajen yin amfani da jami’an Hukumar Tsaro ta kasa (SSS) a kama malamin nasu a bara, inda suka bukaci hukumar ta sako malamin ko ta gabatar da shi gaban shari’a, idan akwai laifin da take zarginsa da shi.
Wasu daga cikin almajiran da iyalan malamin a karkashin Malam Suleiman Abubakar ne sun bayyana haka ne lokacin da suka ziyarci ofishinmu a Abuja, inda suka yi zargin cewa ba yadda za a yi a wanke Mai martaba Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar daga zargin sanya a kama malamin, lura da takaddamar da ta auku tsakanin malamin da masarautar Bidda kan mallakar wani masallaci da mahaifin marigayin ya gina.
Sun ce takaddamar ta kai har Babbar Kotun Tarayya da ke Minna ta yanke hukuncin masarautar ta biya malamin diyyar Naira miliyan 22 kan konewa da rushe masa gida da wasu jama’a suka yi bisa daurin gindin masarautar.
Malam Suleiman Abubakar mai kimanin shekara 42, ya ce, tun da aka kame malamin nasu a bara ana azumi na shida ba su kara ganinsa ko jin duriyarsa ba. “Ya gama tafsiri da karfe 10:30 na dare, bayan ya ta fi gida da misalin karfe 12:23 jami’an tsaro na SSS suke iske shi a gida sannan suka tafi da shi da kanensa Muhammad Muhamad Awwal mai shekara 25, sannan suka wuce gidan dalibinsa Zubairu Adam suka tafi da su,” inji shi.
Ya ce, sun sanya lauyansu ya rubuta takardar korafi ga Eriya Kwamanda na Bidda da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Neja da kuma Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya da kuma sojojin atilare, amma babu wata amsa da suka samu.
Da aka tambaye shi ko muke suke zargin ya sa aka kama malamin, sai ya ce, “A iya saninmu babu abin da malaminmu ya yi, amma muna zargin masarautar Bidda da hannu wajen kama shi. Muna zargin Etsu Nupe ne ya sa aka kama mana malami. Dalilin da ya sa muke zargin, shi ne, akwai rashin jituwa da ta faru tsakanin Malam Isah da Etsu Nupe, kan rikicin masallaci da ke gidan Malam Isah.”
Malam Suleiman Abubakar ya kara da cewa, “Al’amarin ya faro ne tun 1997, domin Malam Isah Ahlis Sunnah ne, sai sabani ya hada su da ’yan darika inda kowa ke son mallakar masallacin da mahaifin Malam Isah Gausu a gina a kofar gidansu, musamman a kan wanda zai yi limanci, rikicin ya sa har aka rufe masallacin.”
Ya ce daga baya da al’amarin ya ci tura sai aka nufi Kotun Majistare ta Bidda a lokacin marigayi Estu Nupe Dokta Umar Sanda Ndayako, saboda ’yan darikar unguwar sun ce koda mahaifinsa ne ya gina masallacin, to, masallaci na Allah ne, don haka tunda su suka fi yawa a unguwar dole masallaci ya zama nasu. “Daga farko kotu ta yanke hukuncin bangaren Malam Isah ya rika limanci, bayan rikicin ya dauki sabon salo, sai kotun ta yanke hukuncin a rufe masallacin, inda kuma aka rufe har tsawon shekara biyu,” inji shi.
Malam Suleiman ya ce “Kotun ta nada liman daga bangaren Malam Isah, Na’ibi daga bangaren ’yan darika. Amma a ranar ’yan darika suka tayar da kayar baya, suka ce sam ba su yarda ba, dole sai an ba su masallaci domin sun fi yawa, aka fara rikici shi ne aka rufe masallacin, kuma shekara biyu bayan hakan Allah Ya yi wa Etsu Umaru Sanda rasuwa.”
Ya ce “Da aka nada Alhaji Yahaya Abubakar a matsayin sabon Sarki, bai yi bincike a kan al’amarin ba, da rana tsaka ya tura hakimi a bude masallacin kuma a danka shi ga hannun ’yan darika. A wurin bikin bude masallacin ne Malam Isah ya ce bai yarda ba, domin ba Sarki ne ya rufe masallacin ba, kotu ce, kuma a dokar kasar kotun ce kawai take da ikon bude masallacin, ya yi wa hakimi bayani shi kuma ya koma wurin Sarki. Bayan nan ba mu ji wani abu daga fada ba, amma dai masallaci an bude, sai wanda kotu ta nada limanci ya ci gaba da Sallah.”
Ya ce, bayan kamar wata uku sai ’yan darika suka zo gidan Malam Isah suka tayar da rikici, suka kone tare da rushe gidan, daga baya Malam Isah ya nufi Babbar Kotun Tarayya da ke Minna, suka bayar da sunayen wadanda suke zargi da hannu a ciki, su Ashirin da wani abu, kotu ta ba su sammaci, su kuma suka je wurin Etsu Nupe ya karbi sammacin ya ajiye ya kuma ce kada su je kotun.
Malam Suleiman ya ce ranar zuwa kotu sai Etsu Nupe ya tura lauyoyin fada. Aka gudanar da shari’a, alkalin kotun na lokacin Malam Yahuza ya yanke hukuncin masarautar Bidda ta biya Malam Isah Naira miliyan 22, kuma jaridun The Nation ta ranar 28 ga Afrilun 2010 da Daily Trust duk sun buga labarin.
Ya ce Etsu Nupe ya daukaka kara a Kotun daukaka kara ta Abuja, amma kotu ta kori kararsa. “Kwana uku bayan an kori karar ne aka kama Malam Isah da kanensa da dalibinsa da ke tafiyar da harkokin shari’ar. Yau shekara ke nan ba mu kara ganinsu ba,” inji shi.
Suleiman Abubakar ya ce sun je wurin liman kan kame malamin da almajirinsa, shi kuma ya samu Etsu Nupe da shugaban karamar hukuma amma suka ce ba su san da maganar ba. “Mun rubuta takardu da dama kan bacewar malaminmu tarde da zargin Hukumar SSS da hannu kan kame shi ta hannun lauyanmu Akingbade Oyelekan na Ultimate Chambaers, kamar wadda muka aika ga Daraktan Hukumar SSS na Jihar Neja ranar 3 ga Agustan 2012 da Majalisar Dokoki ta Jihar Neja a ranar 27 ga Agustan 2012 da kuma shigar da karar Hukumar SSS a Babbar Kotun Tarayya da ke Minna kan tsare malamin, amma kotun ta sallami karar saboda mun kasa gabatar da shaidar da za ta nuna Hukumar SSS ne ta kame malamin namu.”
Malam Sualiman Abubakar ya ce, ana cikin hakan ne sai kwanan nan wani da ya fito daga tsaron da aka yi masa a Hedkwatar SSS da ke Abuja, ya zo Bidda ya fada musu cewa Malam Isah ya turo shi cewa a gaya musu yana tare da SSS a hedkwatarsu, alhali a baya da lauyanmu ya same su sun ce ba su suka kama shi ba.
Ya ce, jin haka ne ya sanya suka sake rubuta takardar kuka ga Babban Lauyan Jihar Neja kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Neja a ranar 27 ga Maris, 2013 suna bayanin yadda jami’an SSS suka zo neman malamin a ranar 25 ga Yulin, 2012 inda suka iske kanensa Usman Mohammed wanda ya shaida musu Malam Isah ba ya nan, sai suka ajiye lambar wayarsu suka ce za su dawo. Kuma da misalin karfe 12:15 na dare suka dawo gidan malamin suka yi awon gaba da shi.
Sun ce jami’an na SSS sun gayyaci wani mai suna Malam Bulala inda suka yi masa tambayoyi a kan dangantakarsa da wanda ke tsaren, lamarin da ya sanya suka sanya ran gano inda yake, amma a karshe fatarsu ta kwaraneye ba tare da faruwar wani abu ba.
“Mun shigar da kara amma kotu ta kori karar tun da ba mu da kwararan hujjoji da suka nuna cewa Malam yana tsare a wurin SSS. Shi ne muke so duniya ta san halin da ake ciki. Ga batun masallaci kuma har yanzu mutanen Malam Isah suna Sallah, kuma Etsu Nupe ya ki biyan diyyar.
daliban wadanda suka zargi Etsu Nupe da sanyawa ana tsare almajiran malamin a wani kurkukunsa da ake kira Kogon Giwa sun ce biyu daga cikin daliban Malam Isah Gausu, Malam Muhammad Umar da Ndagi Sokolobe suna daga cikin almajiransa da fadar Etsu Nupe ta kama kulle tare da yi musu gwale-gwale.
Etsu Nupe bai da hannu kan kama Isah Gausu -Sakatare
Daga Muhammad danladi Ibrahim, Minna da Misbahu Bashir
Malam Abdul-Malik Usman shi ne Sakataren Masarautar Bidda, lokacin da Aminiya ta tuntube shi kan zargin da dalibai da iyalan Malam Isa Gausu ke yi ga Mai Martaba Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar cewa yana da hannu game da kamawa da ci gaba da tsare malamin ya nuna mamaki kan yadda wannan labarin ke ta yawo a gari. Ya ce Masarautar da Mai martaba Etsu Nupe ba su da masaniya a ranar da al’amarin ya faru sai washegari suka ji ana ta yada labari a gari.
Sakataren ya ci gaba da cewa a ranar da aka kama malamin da wani amininsa, yana kan hanyarsa ta komawa gida ne daga ofis yayin da ya hadu da motocin jami’an tsaro a kan hanya. Sun tsayar da shi aka kuma duba motarsa kamar yadda ake yi wa kowane abin hawa, yadda aka saba a duk fadin kasar nan, musamman idan ana hasashen wani abu yana iya faruwa da zai iya tayar da hankalin jama’a.
Ya ce duk da a shekarun baya an samu matsala tsakanin almajiran Malam Isah Muhammad Awwal da ’Yan darika da ta kai ga asarar dukiya. Mai Martaba Etsu Nupe ya shiga tsakani inda ya nemi bangarorin su kai zuciya nesa a ci gaba da zama lafiya don masarautar ta samu c igaban da ake bukata. Wannan ne ya sa ya kafa kwamitin da Shugaban karamar Hukumar Bidda Malam Mustapha Umar Edota ya shugabanta ya auna irin asarar da aka yi, tare da neman gwamnatin Jihar Neja ta taimaka wa wadanda suka yi asarar dukiya.
Sakataren ya ce Mai martaba Etsu Nupe mutum ne da ya yarda da akidar zaman tare, ba tare da nuna bambancin addini, ko shiyya ba, tun daga lokacin da Allah Ya dora masa nauyin jan ragamar Masarautar Bidda a matsayinsa na Sarki. Ya ce Etsu ya nuna kofa a bude take ga duk wanda zai bayar da shawarwari masu ma’ana don a samu biyan bukata.
Dangane da dakin adana jama’a da ake ikirarin Etsu Nupe yana tsare jama’a kuwa, Sakataren ya nuna takaici kan yadda jama’a za su zauna su shirya labarin da babu kanshin gaskiya a ciki, sai ya nuna wa wakilinmu dakin da ke jikin wani dadadden fadar Sarkin da aka yi ta amfani da shi a matsayin dakin wakafi bisa tsarin masarautun Arewa da Ssarakuna suke hada ayyukansu da limanci da alkalanci a baya, inda a duk lokacin da ake da bukatar ajiye mutum nan ake sa shi har sai an idar da shari’ar da ta shafe shi.
Aminiya ta lura cewa dakin ya dade rabon da a yi amfani da shi wanda wannan wata alama ce da ta nuna ba a amfani da shi a matsayin wurin tsare jama’a a fadar yadda ake yayatawa a gari.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi kakakin Hukumar SSS ta kasa, Marylin Ogar ba ta dauki wayar da ya buga mata don tabbatar da zargin ko musanta shi ba, kuma ba ta mayar da amsar sakon tes da ya aika mata ba tun ranar Larabar makon jiya.