Daliban jami’a sun kashe abokinsu saboda wayar salula a Oyo
Daliban sun zargi Alex Akpo da satar wayar salula ne da ya yi amfani da ita wajen tura sakon kudin cacar wasanni
Jami’ar Ajayi-Crowther da ke Jihar Oyo ta fara zaman makoki da azumi da addu’o’in juyayin mutuwar wani dalibinta mai suna Alex Akpo Timiley wanda wasu daliban makarantar suka lakada wa duka har ya mutu a ranar Juma’a da ta gabata.
Daliban sun zargi Alex Akpo da satar wayar salula ne da ya yi amfani da ita wajen tura sakon kudin cacar wasanni, suka yanke wa kansu wannan danyen hukunci.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani Mataimakin Shugaban Jami’ar ta Ajayi-Crowther, Farfesa Timothy Adebayo, ya ce yanzu haka sun kama dalibai 20 da ake zargi da hannu wajen kisan Alex mai shekaru 22 da ke aji 200 a fannin Mechanical Engineering.
Ya ce binciken da suka gudanar sun gano cewa bayan mika daliban ga ’yan sanda sun tabbatar da cewa ana ci gaba da tsare 12 daga cikin su.
- Najeriya ta koma amfani da tsohon taken kasarta
- Zargin Ta’addanci: Kotu ta sallami Shugaban Miyetti Allah Bello Bodejo
Farfesa Adebayo wanda ya ce ya shafe kwanaki biyu yana kukan juyayin mutuwar wannan dalibi, ya ce hukumar makarantar ta dauki tsauraran matakan dakile aukuwar irin haka a nan gaba.
Gwamnatin Jihar Oyo ta yi kira ga bangarorin da wannan lamari ya shafa su kwantar da hankali domin samun damar gudanar da binciken kwakwaf a kan matsalar.
Kwamishinan ilmi na Jihar Farfesa Salihu Adelabu ne ya yi wannan kira a ranar talata cikin wata Sanarwa.