Daliban Japan sun koka da kudin abinci Naira 512,919.5 a Italiya

Wasu dalibai da suka shiga gidan sayar da abinci an caje su £1,004, wato sama da Naira dubu 500 kan tsinkayen tsiren kifi hudu da ruwan kwalba mai sinadarai, don haka suka sanar da ’yan sandan Italiya vorafinsu kan lamarin. daliban dai sun fito ne daga vasar Japan, inda suka kai ziyara benice sai aka […]

Daliban Japan sun koka da kudin abinci Naira 512,919.5 a Italiya

Wasu dalibai da suka shiga gidan sayar da abinci an caje su £1,004, wato sama da Naira dubu 500 kan tsinkayen tsiren kifi hudu da ruwan kwalba mai sinadarai, don haka suka sanar da ’yan sandan Italiya vorafinsu kan lamarin.

daliban dai sun fito ne daga vasar Japan, inda suka kai ziyara benice sai aka ba su takardar biyan kudin abincinsu a gidan sayar da abinci na Ostera da Luca da ke daura da dandalin St. Mark a birnin benice da ke vasar Italiya, kamar yadda jaridar Mirror ta ruwaito.

Sai dai ba a tantance kan ko cewa daukacin daliban sun biya kudin abinci, domin a cewar Luigo Brugnaro Magajin gari benice ya yi alvawarin bin kadin lamarin.

Sai dai mai gidan abincin ya bayyana cewa ba zai iya tuna cewa ko ya taba samun wata matsala da dalibai daga vasar Japan ba.

Wata matsalar da ta taba aukuwa shigen irin ta daliban Japan, ita ce ta masu yawon bude idanu daga vasar Birtnaiya, wadanda aka damfare su har suka biya kudin abinci na fam £463, wato kimanin Naira 231,500 a wani gidan abincin Italiya mai sunan Trattoria Casanoba da ke birnin benice.

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu