daliban Kwalejin Ilimi a Gombe sun koka da rashin ruwa
Da yammacin Talatar da ta gabata ce dubban daliban Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Gombe suka yi koka a gaban Ministan Ilimi saboda rashin ruwan fanfo a kwalejin na tsawon wasu kwanaki da hakan ya haifar musu da matsalar rashin wanka da dafa abinci.daliban sun koka ne da katsewar ruwan fanfo da kuma […]
Da yammacin Talatar da ta gabata ce dubban daliban Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Gombe suka yi koka a gaban Ministan Ilimi saboda rashin ruwan fanfo a kwalejin na tsawon wasu kwanaki da hakan ya haifar musu da matsalar rashin wanka da dafa abinci.
daliban sun koka ne da katsewar ruwan fanfo da kuma wutar lantarki a sashin kwalejin, musammam ma a ginin rukunin ‘B’ da hakan ya tunzura su har suka dinga yi wa Ministan Ilimi Ibrahim Shekarau ihun cewa ‘ba ruwa, ba ruwa!’ a lokacin da ya kai ziyarar aikin kaddamar da wasu gine-gine da kwalejin ta gina.
daliban sun yi ihu ne domin ministan na ilimi ya ji kukansu, ko za a gaggauta daukar matakin shawo karshen matsalar, wanda suka ce rashin ruwan ya sa da yawansu ba su iya yin wanka har na tsawon kwanaki uku.
daliban sun shaida wa wakilinmu cewa kafin wannan rana, sun kai kokensu ga hukumar al’amuran dalibai amma al’amarin ya ci tura, inda suka kara da cewa tun da aka dawo zangon karatu na biyu ne suke fama da rashin wuta sannan yanzu rashin ruwa ya biyo baya.
A lokacin da yake ganawa da daliban, ya amsa wata tambaya daga wata dalibar sashin koyon harsuna a kan rade-radin da suka ce ana yi, cewa za a canja wa jami’ar matsugunni daga garin kashere, inda Malam Shekarau ya tabbatar musu da cewar a matsayinsa na Ministan Ilimi, babu wani abu kamar haka.