daliban makarantar Glisten sun fafata a gasar wasannin motsa jiki
Makarantar Glisten International da ke Abuja ta gudanar da gasar wasannin motsa jiki a tsakanin dalibanta inda daliban da ake kira Europe House suka lashe gasar a matakai daban-daban.daliban da ake yi wa lakabi da Asia House su ne suka zo na biyu sai daliban da ke wakiltar Amurka wato America House suka zo na […]
Makarantar Glisten International da ke Abuja ta gudanar da gasar wasannin motsa jiki a tsakanin dalibanta inda daliban da ake kira Europe House suka lashe gasar a matakai daban-daban.
daliban da ake yi wa lakabi da Asia House su ne suka zo na biyu sai daliban da ke wakiltar Amurka wato America House suka zo na uku sai kuma daliban da ake yi wa lakabi da Africa Housa suka zo na karshe.
Da yake jawabi jim kadan bayan kammala gasar, dalibin da ke wakiltar Europe House da suka zama zakara, Zainab Ahmed ta ce hadin kan da ke tsakanin ’yan wasansu ne ya ba su damar samun nasara.
“Gaskiya na yi mamakin ganin yadda ’yan garinmu suka hada kai suka cimma burin da suka sanya a gaba”. Inji ta
Ta bayyana cewa za su ci gaba da bayar da himma wajen ganin sun sake lashe gasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.
Ita kuwa Maryam Wowo wadda ta wakilci daliban da suke kiran kansu da Africa Housa wato gidan Afirka ta bayyana cewa faduwar da suka yi a gasar ya tilasta musu sun gano kurakuran da suka tafka.
Ta bayyana cewa za su gyara kurakurensu don tunkarar kalubalen da ke gabansu a gasar da za a yi nan gaba.
Shi ma Is’hak Baffa wanda ya wakilci Gidan Asiya wato Asia House ya yaba wa ’yan wasansu da suka zo na biyu a gasar.
Shugaban sashen sakandare na makarantar, Eneh Cherles, ya ce sun shirya gasar ce don karfafa gwiwar dalibansu kan wasannin motsa jiki.
Ya ce gasar za ta baiwa daliban damar su samu karin gogewa tare da sanin makamar yadda ake fafatawa don samun nasara.
Ita ma shugabar sashen makarantar firamare, Misis Prisca Godwill, ta bayyana cewa gasar za ta taimakawa daliban wajen bunkasa fasahar da suke da ita a fannin wasanni.
Ta ce daliban sun nuna bajinta da kwarewa ta musamman kuma gasar ta ba su damar yin fice a tsakanin takwarorinsu.
Ta yi kira ga iyayen yaran makarantar su ci gaba da tallafawa yaran a fanin wasannin don cimma burin da suka sanya a gaba na zama zakaru.