daliban Makarantar Kiwon Lafiya ta Gwadabawa sun koka kan karacin wurin kwana

daliban Makarantar Koyon Kiwon Lafiya da ke Gwadabawa a Jihar Sakkwato sun bukaci Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya samar musu da karin dakunan kwana saboda dakunan da ke cikin makaratar sun yi musu kadan.A ziyarar da Aminiya ta kai makaratar dalibai maza da mata sun roki Gwamna Tambuwal ya samar musu da […]

daliban Makarantar Kiwon Lafiya ta Gwadabawa sun koka kan karacin wurin kwana
daliban Makarantar Kiwon Lafiya ta Gwadabawa sun koka kan karacin wurin kwana

daliban Makarantar Koyon Kiwon Lafiya da ke Gwadabawa a Jihar Sakkwato sun bukaci Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya samar musu da karin dakunan kwana saboda dakunan da ke cikin makaratar sun yi musu kadan.
A ziyarar da Aminiya ta kai makaratar dalibai maza da mata sun roki Gwamna Tambuwal ya samar musu da karin wurin kwanciya.
Bashar Abdullahi dalibi a fanin koyon tsabtar muhali a makaratar ya ce, “A baya muna fama da matsaloli sosai amma a yanzu shugaban makaratar ya magance galibin matsalolin, abu daya muke fama da shi rashin wurin kwanciya don haka muke kira ga gwamnati ta taimaka mana domin muna shan wahala sosai.”
Shi ma Ubaida Sani da ke fannin kiwon lafiya a karkara ya tabbatar da wannan batu, inda ya ce dakin da ya kamata mutum biyu ne a cikinsa amma sai a samu mutum shida zuwa takwas ke matse a ciki. “Walllahi ba za ka tausaya mana ba sai ka ga yadda muke kwanciya, a kowane daki gado biyu ne amma haka wasu ke hade su wuri daya mutum hudu su kwanta wasu kuma suna karkashin gadon,” inji shi.
Ya ce tunda makarantar tana da isasshen wurin gini ya kamata gwamnati ta kai dauki na gina sababbin wuraren kwana domin tana da ruwa da wutar lantarki.
Da wakilinmu ya tuntubi Daraktan Makarantar Alhaji Nasiru Aliyu ya tabbatar da cewa makaratar na fama da karancin wuraren kwanan dalibai “dalibanmu na fama da karancin wurarern kwanciya, saboda haka sai da muka fita cikin gari muka samar da gidajen haya muka daukar wa daliban domin ba inda za mu aje su, kuma don saukaka wa daliban muka gyara motoci biyu domin kai su gidajen da muka tanadar masu da dauko su,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Na sanar da gwamnati kan wannan matsala, kuma Mai girma Gwamna ya tabbatar min a bana za a magance matsalar, don haka ina kira ga daliban kara hakuri mun dauko gyaran makaratar kuma za mu bakin kokarinmu kan gyara ta,” inji shi.