Daliban makarantar kwana sun mutu bayan cin abinci
Biyu daga cikin uku na daliban makarantar sakandaren kwana ta mata da ke unguwar Manga a Danko-Wasagu a jihar Kebbi sun rasu bayan cin abinci mai miyar ganye. A yanzu haka an kafa kwamitin bincike daga Gwamnatin jihar. Daliban da suka ci abincin su ne: Salomi Hassan da Anne Ishaya da Eunice Musa, sun rasu […]
Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu
Biyu daga cikin uku na daliban makarantar sakandaren kwana ta mata da ke unguwar Manga a Danko-Wasagu a jihar Kebbi sun rasu bayan cin abinci mai miyar ganye. A yanzu haka an kafa kwamitin bincike daga Gwamnatin jihar.
Daliban da suka ci abincin su ne: Salomi Hassan da Anne Ishaya da Eunice Musa, sun rasu ne bayan da iyayen wata daliba kawarsu ta kawo masu abincin, daya daga cikin wanda taci abinci mai suna Abigail Benjamin bata rasu ba.