Daliban Najeriya da suka isa Port Sudan za su iya hawa jirgin sama

’Yan Najeriya da suka makale sun shiga kasar Masar, wadanda suka je Port Sudan sun samu masauki, amma babu tabbacin yadda za a kwaso su

Daliban Najeriya da suka isa Port Sudan za su iya hawa jirgin sama

’Yan Najeriya da suka isa Port Sudan bayan tsere wa yaki a Khartoum sun bayyana cewa jirgin sama na iya daukar su daga nan zuwa Abuja.

Dalibai da sauran ’yan Najeriya da aka kwashe daga Khartoum bayan barkewar yaki sun isa Port Sudan ne da misalin karfe 1.30 na ranar Talata, bayan tafiyar sama da awa 12.

Wani dalibi daga cikinsu ya shaida wa Aminiya cewa, “A cikin hostel na maza aka sauke mu, wasu kuma a masallatai wasu kuma sun fita sun kama otel da sauransu.”

Ya ce zuwa safiyar Laraba, babu wata kwakkwarar magana game da yadda dawowarsu, Najeriya, amma ana tunanin daga Port Sudan kai-tsaye za a kwaso zuwa Najeriya, ko kuma sai sun tsallaka ta jirgin zuwa birnin Jiddda na kasar Saudiyya kafin a dawo da su gida.

“Maganar tafiya kuma gaskiya ba su fada mana yaushe za a tafi ba, amma sun ce an ba su izinin amfani da jirgi.

“Akwai airport a nan garin (Port Sudan), wata kila kawai jirgi za a kawo daga Najeriya mu tafi ba tare da an shiga Jiddan ba. Ko kuma a shiga Jiddan ta jirgi ruwa.

“Haka dai muke tunani, daya daga nan cikin hakan zai tabbata gare mu in sha’a Allah,” in ji dalibin, wanda kammala karatun aikin likita a Sudan.

A gefe guda kuma, daukacin rukunin farko na ’yan Najeriya da suka makale a kan iyakar kasar Masar bayan barkwar yaki a Sudan sun samu shiga Masar, bayan kwanaki ba tare da samun izini.

A ranar Talara Shugaban Hukumar Kula da ’Yan Najeriya a Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewa, “An ba wa matata fifiko a yayin da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Masar ya tsallakar da daukacin ’yan Najeriya ke kan iyakar kasar Masar.

“Ana shirin kwaso su zuwa Abuja daga filin jirgin sama da ke Aswan, kuma har Jirgin Air Peace ya sauka.”

Idan za a iya tunawa, kamfanin Air Peace ya sadaukar da jiragensa domin kwaso ’yan Najeriyan da suka makale, da zarar sun fice daga Sudan.

Hakazalika, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tura jiragenta guda uku domin kwaso ’yan Najeriya da yakin Sudan ya riske su, bayan tsallakawa zuwa kasar Masar.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno