daliban Poly takwas ne suka rasu a harin bam din Masallacin Jambutu
Hukumar Kwalejin Poly da ke Jihar Adamawa ta ce ta rasa dalibanta takwas a harin bam din da ya auku a masallacin Juma’a na Jambutu.Bam din ya tashi ne a lokacin da ake walimar bude masallacin wanda ke kusa da ajujuwan masu karatun zama injiniya a ranar Juma’ar da ta wuce.An tabbatar da faruwar hakan […]
Hukumar Kwalejin Poly da ke Jihar Adamawa ta ce ta rasa dalibanta takwas a harin bam din da ya auku a masallacin Juma’a na Jambutu.
Bam din ya tashi ne a lokacin da ake walimar bude masallacin wanda ke kusa da ajujuwan masu karatun zama injiniya a ranar Juma’ar da ta wuce.
An tabbatar da faruwar hakan ne a lokacin da kakakin Kwalejin, Albert Matilah ya yi wa manema labarai bayani a game da faruwar al’amarin.
Matillah ya nuna cewa daga cikin dalibai su kimanin ashirin da biyar da suka ji rauni a lokacin harin bam din, yanzu dalibai hudu ne ke kwance a asibiti suna karbar magani.
Ya ce bayan harin bam din, hukumar makarantar ta tsaurara matakan tsaro inda ake gudanar da bincike ga duk masu shiga da kuma fita daga cikin kwalejin don hana aukuwa haka nan gaba.
Ya ce sakamakon harin ya sa hukumar kwalejin ta bayar da hutun kwana biyu don a samu sukunin yi wa wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata addu’a. Ya ce hukumar makarantar ta dauki alkawarin taimakon masu jinya a asibiti da kudin magani musamman wadanda ke kwance a asibitin kwararru na Jami’ar Yola (FMC).
Ya hori daliban da suka cigaba da sanya ido, da zarar suna shakkar wani ko wasu, to su yi saurin sanar da hukumar tsaro na makarantar don a dauki matakin gaggawa.
Hukumar makarantar ta yi alkawarin kai ziyarar ta’aziya gidajen daliban da suka rasa rayukansu.