Daliban Sheikh Dahiru Bauchi 2,664 sun sauke Alkur’ani
An yi wa mahaddada sama da 2,000 da wadanda suka yi sauka addu’a ta musamman.
Daliban da ke karatu a ciki da wajen Najeriya a karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, 2,664 ne aka yi wa addu’ar saukar karatun Alkur’ani a Bauchi.
Daga cikinsu dalibai 2,438 sun haddace Kur’ani yayin da 226 suka sauke.
- Jami’an tsaro sun cafke malamin ’yan bindiga a Kaduna
- Mutanen da Buhari ya aminta da su ke yaudarar shi —Solomon Dalung
Jihar Bauchi ce ta fi yawan mahaddata da dalibai 534, sai 226 da suka yi sauka. Jihar Katsina na da dalibai 499 sai Kano 385 suka yi hadda.
Jihar Kaduna ke biye da dalibai 257 sai Jigawa 186 sai jihohin Sakkwato da Zamfara ke da dalibai 168 da 152 mahaddata.
Da yake musu addu’a, Shehu Dahiru Bauchi ya ja hankalin daliban su kara zage damtse domin inganta tilawarsu, inda ya ce Alkur’ani abu ne da in mutum ya sauke ko ya haddace ana so kullum ya rika bibiyarsa yana yawan karantawa.
Shehin wanda babban dansa Ibrahim Sheikh Dahiru ya wakilce shi ya ce makarantar tana da hadin gwiwa da Jihar Neja kan yadda za a karafafa haddar Alkur’ani a makarantun jihar.
Gwamna Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya nanata kudirin gwamnatinsa na inganta ilimi a jihar, sannan ya gode wa Sheikh Dahiru Bauchi saboda addu’o’in zama lafiya da yake yawan yi wa kasa.
Gwamnan wanda Kwamishinan Ma’aikatar Addinai Alhaji Umar Babayo Kesa ya wakilta, ya nanata kudirin gwamnatinsa na taimaka wa makarantun addini sai ya roki jama’a su yi koyi da halayen Annabi Muhammadu (SAW), ta hanyar hakuri da juna da sadaukar da kai da zama lafiya.
Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello wanda ya turo wakilcin Babbar Jami’arsa Hajiya Halima Idris ya ja halin wadanda suka yi karatun su kara himma domin karatun ya zauna sosai yadda ya kamata.
Shugaban Taron, Sarkin Zungur, Alhaji Sa’idu Hamidu Bello, ya nanata muhimmancin karatun Alkur’ani wanda ya ce shi ne sababin shiriya ga al’umma kuma shi ne abin da yake jawo wa dan Adam alheri a duniya da Lahira.