Dalibar da aka yi wa sharrin safarar kwayoyi zuwa Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA
Bayan shekara biyu da wanke Zainab ta kammala karatu ta kuma zama hafsa a NDLEA
Zainab, matashiyar nan ’yar Kano da aka taba tsarewa a kasar Saudiyya kan zargin safarar miyagun kwayoyi, ta zama jami’ar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA).
A halin yanzu, Zainab na daga cikin sabbin hafsohin NDLEA 2,000 da aka yaye ranar Juma’a bayan sun kammala samun horo a kwalejin horas da kananan hafsoshin hukumar.
- Zulum ya raba wa ’yan gudun hijira N500m da kayan masarufi
- Mun dora daga inda Ali Kwara ya tsaya —Halifansa
A shekarar 2019, lokacin Zainab tana aji uku a jami’a, matashiyar ta shiga tsaka mai wuya a lokacin da ta tafi aikin Umrah a kasar Saudiyya.
Saukarta a filin jirgi a kasar Saudiyya ke da wuya aka tsare ta bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Kasar Saudiyya dai kan zartar da hukuncin kisa ga duk wanda ta kama da laifin fataucin miyagun kwayoyi.
Halin da Zainab ta shiga a lokacin ya tayar da hankalin iyayenta da abokan karatunta da sauran jama’a, wadanda suka yi ta bayar da kyakkyawar shaida a kanta.
Daga baya gwamnatin Najeriya ta shiga cikin lamarin da nufin gano gaskiya, duba da irin kyakkyawar shaidar da dalibar ta yi ta samu.
A yayin bincike ne daga baya aka gano cewa wasu bata-garin ma’aikatane suka cusa kwayoyin a jakarta a Filin Jirgi na Malam Aminu Kano da ke Kano, ba da saninta ba, a hanyarta ta zuwa Saudiyya domin yin ibadar Umrah.
Daga baya hukumomin kasar Saudiyya suka wanke ta daga zargin, ta dawo Najeriya ta ci gaba da rayuwarta ta kuma kammala karatunta.
Bayan kammala karatun nata ne a halin yanzu ta samu aiki kuma tana daga cikin sabbin hafsoshin hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da aka yaye a wannan makon.