Dalibar da ke kai wa ’yan bindiga rahoto ta shiga hannu

Dalibar ta amsa cewa ita budurwar wani dan bindiga da ake nema ruwa a jallo ne kuma ta kai masa bayanai

Dalibar da ke kai wa ’yan bindiga rahoto ta shiga hannu

An cafke wata dalibar Kwalejin Kiwon Lafiya da ke Kontagora, kan zargin ta da kai wa ’yan bindiga bayanai a Jihar Neja.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Neja, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya ce an cafke dalibar da ke karatu a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da ke Kontagora ne bayan an kama wani dan bindiga mai shekara 37.

A yayin binciken dan bindigan da aka kama a garin Kontagora ne aka gano lambar dalibar a cikin wayarsa.

Ita kuma a wurin bincike aka gano sunan wani dan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Shaibu Haruna a wayarta, da suna ‘Kudin-banza’.

A cewar kwamishinan ’yan sandan, dalibar ta amsa cewa wata mata ce ta hada ta da Shaibu, wanda take kai wa bayanai kuma yake lalata da ita.

Kwamishinan ’yan sandan ya ce shugaban ’yan bindigar da ya shiga hannu ne ya bayar da lambobin wasu guda biyu daga cikinsu Maidabo da Shaibu Haruna na garin Garatu, a Karamar Hukumar Bosso.

Shawulu Ebenezer ya ce an kama wasu mutum biyu kuma mazauna garin Salka da ke Karamar Hukumar Magama da ake zargi da alaka da ’yan bindiga.

Ya ce rundunar ’yan sandan ta bankado yadda ’yan bindigar suka aike wa mutanen biyu Naira 10,000 ta POS a garin Salka.

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7