Dalibar jami’a na yin barcin mako uku a lokaci guda

… ‘Wadansu na kirana malalaciya saboda yawan barci’ • Dalibar tana barcin sa’a 22 kullum • An kore ta daga aji saboda rashin rubuta jarrabawa • Duk da likitoci sun ce tana da cutar barci wadansu ba su daina kiranta malalaciya ba   Wata dalibar jami’a ta  mai suna Rhoda Rodriguez-Diaz ta bayyana yadda take […]

Dalibar jami’a na yin barcin mako uku a lokaci guda

Dalibar jami’a na yin barcin mako uku a lokaci guda

… ‘Wadansu na kirana malalaciya saboda yawan barci’

• Dalibar tana barcin sa’a 22 kullum

• An kore ta daga aji saboda rashin rubuta jarrabawa

• Duk da likitoci sun ce tana da cutar barci wadansu ba su daina kiranta malalaciya ba

 

Wata dalibar jami’a ta  mai suna Rhoda Rodriguez-Diaz ta bayyana yadda take fama da larurar yawan barci, inda take barcin makonni a lokaci guda, a wani lokacin kuma tana yin barcin ne a daidai lokacin da take rubuta  jarrabawa a makaranta.

Daliba Rhoda Rodriguez-Diaz, budurwa mai shekara 21, da zaune a birnin Leicester na kasar Ingila, ana yi mata lakabi da  ‘Kyakkyawa mai ciwon barci’ inda  take yin barcin sa’o’i 22 a kowace rana, kuma tana farkawa ne kawai kamar a mafarki ta ci abinci ta sha abin sha sai kuma ta shiga ban-daki.

Akalla barcin Rhoda wani lokacin yana kaiwa mako uku, wanda hakan ya sa ta fadi a jarrabawar jami’a na zangon karatu guda a shekara ta biyu, a wannan lokacin tana ta barci har aka kammala jarrabawar.

Rhoda, ta ce “Ina matukar jin kunya idan jama’a suka kira ni da sunan malalaciya a koyaushe ina kokarin in magance yadda zan gusar da wannan suna saboda kin sa da nake yi.

Amma ina kokarin kada wannan suna ya shafi wasu harkokin rayuwata. Wannan barci na halitta ne, ba ni na sa wa kaina ba. Abin damuwa ce matuka ba yadda zan yi ne kawai.”

Tun Rhoda tana yarinya aka yi mata gwajin cuta a asibiti aka gano tana dauke da cutar da take sanya ta kasala.

A watan Satumba bara ne likitoci suka binciko larurar da take damun kwakwalwar Rhoda, inda suka ce a duk cikin mutum miliyan daya ana iya samun mai irin wannan cutar barci mutum daya da ake kira ‘Kleine-Lebin Syndrome.’

Rhoda ta dade tana fuskantar wannan larura ta barci, amma idan akwai hutun makaranta ba ta da wani aikin da yawu ce ta yi ta barci.

“Ina ci gaba da rayuwa lokacin da nake barci. Idan har na farka bayan na fahimci cewa, na yi asarar mako daya na rayuwa abin yana damuna.” inji Rhoda.

“Ina matukar jin zafin abubuwan da suka wuce ni lokacin da nake barci. Wannan shi ne abu mai wahala da nake fuskanta. Yana da wuya in iya bayyana wa jama’a halin da nake ciki, saboda kalilan ne za su fahimta,” inji ta.

Rhoda ta bayyana takaicinta idan ta tuna lokacin da take yarinya kasancewar ba ta hulda da sauran kawayenta, saboda rashin lokacinsu da ba ta da shi, ta so a ce tana hulda da sauran kawayenta.

Rhoda ta ce, “Lokacin da nake ’yar shekara hudu zuwa biyar, ina barcin mako biyu zuwa uku a lokaci guda wanda hakan ya sa likitan da yake duba ni ya gaza gane abin da ke damuna.”

“Wannan barcin ya fi yawa lokacin ina karama. Amma bai sake faruwa ba, sai da na zama budurwa. Ina tuna lokacin da nake da shekara 15 zuwa 16 na samu kaina cikin halin yawan barci, idan ina makaranta barci yana damuna haka idan ina wajen karatu. Ina matsa wa kaina ne in je makaranta, ba na jin dadin yadda nake kasancewa cikin barci a koyaushe, ina  tilasta wa kaina ne kawai,” inji Rhoda.

Dalibar ta kara da cewa, “Wani lokacin ina motsa jiki, amma duk lokacin da na yi nakan ji gajiya. Ina matsa wa kaina wajen gudanar da wasu harkokin yau da kullum amma sai in kasance cikin kasala a koyaushe, har sai na farka nake jin yanayin jikina ya yi min dadi. Kawayena su kansu ba su iya tantance yadda yanayina ya sauya wata rana ina tashi sai duk al’amurana su sauya.”

Rahotanni sun ce, daga watan Fabrairu zuwa Yunin bara, Rhoda ba ta samun cikakken lokacin karatu ba.

Halayyar Rhoda na yawan barci ya sa aka kore ta daga darasin da take yi a watan Yuli, saboda yawan jarrabawar da ba ta samu ta yi ba har lokacin jarrabawar ya wuce saboda tana ta barci lokacin da ake rubuta jarrabawar.

Bayan Rhoda ta ziyarci malaminta, sai ya shawarce ta kan ta je asibitin St Thomas daga nan aka yi mata gwajin abin da ke damunta a watan Satumba.

Rhoda ta bayyana wa likitan asibitin cewa, da farko ba ta dauki yawan barcin a matsayin mai cutarwa ba, sai daga bisani ta fahimci cewa, yawan barcin na kawo mata koma-baya a harkokinta don haka ta ziyarci likita.

A lokacin da Rhoda ta ziyaci malaminta ta nuna masa cewa, ba da gangan ba ne take kin yin wasu ayyukan jami’ar, larurar da take tare da ita ce take hana ta yin wasu ayyukan da malaman jami’ar suke ba ta.

Rhoda, ta ce ba ta san yawan barci na yi mata illa ba har sai da ta ziyarci likita a watan Satumban bara.

“Zan iya tunawa a cikin wata uku da suka wuce, na yi barcin sama da sa’o’i 60 a cikin kwana uku.

Rhoda, ta ce “Na rasa jarrabawa da dama, ban samu damar yin kashi 60 cikin 100 na darussan ba, yayin da ban yi rabin jarrabawar da ya kamata a ce na yi ba. Ba laifina ba ne, yanyin larurar da nake tare da ita ce, ta haddasa min haka. Yanzu haka an ba ni damar maimaita abubuwan da suka wuce na zangon karatun shekara ta biyu. Wannan zai zamar min abu mai wahala.”

Mutanen da suke fama da wannan cuta suna iya rayuwa a yanayin halin da suke ciki, Rhoda kuwa ta kasance larurar yawan barcin nata ya yi kamari lokacin da take budurwa.

“Na san cewa, ina da yawan barci wani lokacin har mafarkin barcin nake yi. Wannan barcin yana kawo min nakasu a harkokin rayuwata, ina fatan ya zamar min tarihi in kasance ina yin abin da zai taimaka wa rayuwata nan gaba,” inji ta.