Dalibar jami’ar Jos ta rasu a dakin daliban jami’ar

Rahotanni  na bayyana cewa, an samu wata dalibar  jami’ar Jos da take karatu a tsangayar koyar da kasuwanci mai suna Mercy Naan ta rasu a dakin daliban jami’ar na Zion Hostel, daki mai lamba 23. Dalibar mai shekaru 23 ta rasu ne tana ajin karatu na shekara ta biyu. A ranar juma’a 3 ga watan […]

Dalibar jami’ar Jos ta rasu a dakin daliban jami’ar

Rahotanni  na bayyana cewa, an samu wata dalibar  jami’ar Jos da take karatu a tsangayar koyar da kasuwanci mai suna Mercy Naan ta rasu a dakin daliban jami’ar na Zion Hostel, daki mai lamba 23.

Dalibar mai shekaru 23 ta rasu ne tana ajin karatu na shekara ta biyu. A ranar juma’a 3 ga watan Mayu 2019, iyayen Mercy Naan suka sanarwa masu gadin jami’ar cewa ‘yar su ta bata ba su san inda take ba.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Filato DSP Tyopev Matthias Terna, ya tabbatar da rasuwar Mercy Naan, ya ce an gano gawar  ne bayan da wasu suka sanar cewa, suna jin wari na fitowa daga dakin da dalibar take.