Dalibi ya lakada wa malamar jami’a dukan kawo-wuka
Ya yi mata jina-jina har ta kai ga an yi gaggawar mika ta asibiti.
Wani dalibin aji hudu a Sashen nazarin kananan kwayoyin halittu (microbiology) a Jami’ar Ilorin, ya lakada wa wata malamarsa dukan kawo-wuka daga neman taimako.
Dalibin da aka bayyana sunansa a matsayin Captain Walz, bai yi kwas din da ya wajaba dalibai su yi ba na samun horo da sanin makamar aiki da ake tura dalibai a shekarar gab da ta karshe ta karatunsu ba wato SIWES, (Students Industrial Work Experience Scheme).
- ’Yan sanda sun ceto dattijo mai shekara 80 da aka sace a Kano
- Iran ta rufe jarida kan alakanta Shugaban Addini na Kasar da talauci
Aminiya ta ruwaito cewa, dalibin ya lakada wa Malamar mai suna Mrs Zakaria dukan tsiya a ranar Alhamis, wadda rahotanni suka ce a karkashin kulawarta ne zai yi bincike da nazari da daliban ajin karshen ke gudanarwa gabanin kammala karatu a jami’a wato Project.
Bayanai sun ce, dalibin ya kai wa malamar ziyara har ofishinta domin neman taimako la’akari da kwas din sanin makamar aiki (SIWES) da bai yi ba.
Sai dai yayin da malamar ta hau kujerar naki da rashin bai wa dalibin hadin kai kan bukatar da ya zo mata da ita, a nan ne ya hau dokin zuciya inda ya yi mata jina-jina har ta kai ga an yi gaggawar mika ta asibiti.
Darektan Kula da Harkokin Gudanarwa na jami’ar, Mista Kunle Akogun, ya tabbatar wa da Aminiya hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da wakilinmu a ranar Asabar.
“Eh tabbas wannan abun takaici ya faru amma a halin yanzu malamar ta farfado kuma tana samun kulawa a asibiti.
“Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdulkareem Age ya kai mata ziyara tare da wasu manyan makarrabai da wasu ma’aikatan jami’ar.
“Sun bayyana lamarin a matsayin abun takaici tare da bayar da tabbacin cewa za a duk wata mai yiwuwa wajen bi mata hakkinta kamar yadda shari’a ta tanada.
“Shugaban jami’ar ya kuma bayar da umarnin a yi wa malamar kyakkyawar kulawa wanda kuma jamiar ce za ta dauk nauyin duk wasu kudade da za a kashe,” a cewar Akogun.