dalibi ya rubuta wa barawon kekensa wasika a Landan

Wani dalibi da aka sace wa keke, ya rubuta wa barawon keken wasika, wai ko ya ji tsoro ya dawo masa da kekensa. Keken Aaron Rush, wani dalibi dan shekara 23, an sace shi a tashar jirgin kasa da ke Landan.A cikin wasikar da ya rubuta wa barawon keken ya ce: “Sannu barawon keke “Hi […]

dalibi ya rubuta wa barawon kekensa wasika a Landan
dalibi ya rubuta wa barawon kekensa wasika a Landan

Wani dalibi da aka sace wa keke, ya rubuta wa barawon keken wasika, wai ko ya ji tsoro ya dawo masa da kekensa. Keken Aaron Rush, wani dalibi dan shekara 23, an sace shi a tashar jirgin kasa da ke Landan.
A cikin wasikar da ya rubuta wa barawon keken ya ce: “Sannu barawon keke “Hi Dbag Bike thief, ka sace mini keke a daren jiya.”
“Sai dai rashin sa’ar da ka yi ita ce, na san inda kake,” inji shi.
Ya ce ya kai rahoton satar keken, amma ’yan sanda sun bayyana masa sai an dauki makonni hudu kafin a kammala bincike.
Tabbas, bincike ya nuna Rush ba shi ne mutumnin farko da ya fara rubuta wa barawo wasika ba. Domin a bara, wani mazaunin Toronto, a kasar Kanada da aka sace mas akeke, ya gano inda barawon ya ajiye, sai shi ma ya sace, sannan ya rubuta wa barawon keken wasika inda ya ce:
“Kai dan iska, ka sace kekena, amma ka ki ka bayyana mini inda ka ajiye shi, to cikin sa’a wani abokina ya gano wurin, wanda dama can shi ne bakanike na. Shin wannan ba wauta ba ce? To ka sani ina bukatar kekena, kuma na dauke shi.

Barau ya buƙaci Ganduje ya ƙwato wa APC ƙarin jihohi

An kama masu laifi 30,000 a 2024 – Sufeto Janar na ’Yan Sanda

DAGA LARABA: Dalilan wasu darikun Kirista ba sa bikin Kirsimeti

PCAACC ta karrama matashin da ya tsinci dala 10,000 a Kano