dalibi ya yi wa mahaifinsa yankan rago

Wani dalibi dake karatun aji uku a Jami’ar RCCG a Jihar Ogun, mai suna Tolani Ajayi, mai shekaru 21 da haihuwa ya kashe mahaifinsa, ta hanyar yankan rago da wuka, ya sanya gawar cikin wani akwati da ya jefar a cikin daji. dalibin ya aikata danyen aikin nasa ne a Talatar  makon jiya a daidai […]

dalibi ya yi wa mahaifinsa yankan rago
dalibi ya yi wa mahaifinsa yankan rago

Wani dalibi dake karatun aji uku a Jami’ar RCCG a Jihar Ogun, mai suna Tolani Ajayi, mai shekaru 21 da haihuwa ya kashe mahaifinsa, ta hanyar yankan rago da wuka, ya sanya gawar cikin wani akwati da ya jefar a cikin daji. dalibin ya aikata danyen aikin nasa ne a Talatar  makon jiya a daidai dandalin Redemption Camp da ke kan hanyar Edpress ta Legas zuwa Ibadan.
 Wata sanarwa da ke kunshe da wannan bayani da ta fito daga rundunar ‘yan sanda a Jihar Ogun, ta ce, an tsinci gawar babban lauya Barrister Charles Ajayi (SAN), mai shekaru 60 da haihuwa ne a cikin wani daji da ke kusa da titin Canaan a cikin kauyen na RCCG.
Sanarwar da Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun, DSP Olumuyiwa Adejobi, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa ‘yan jarida a ranar Lahadin da ta wuce, ya ce, a binciken da ‘yan sanda suka fara yi wa dalibin bayan an kama shi, ya fara yin karyar cewa, mahaifinsa ya tafi zuwa wajen wa’azin kirista da aka saba yi a kauyen na RCCG ne, amma daga baya ya yi wa ‘yan sandan bayani dalla-dalla da bakinsa cewa, matsalar ta faro ne a lokacin da mahaifin na sa ya mare shi, tare da neman sanin dalilin da yasa yake kin amsa addu’o’in da mahaifin ke yi, (shiru yake yi, a maimakon ya ce amin). A daidai wannan lokaci ne ya husata da jin kalaman nasiha da mahaifinsa yayi masa, sai ya garzaya zuwa dakin dahuwar abinci (kicin) ya dauko sharbebiyar wuka ya daba masa, sannan ya nemo adda ya yanke makogwaronsa, al’amarin da ya kai ga mutuwarsa nan take.
 ‘Yan sandan, sun kai gawar marigayin da aka ajiye a Asibitin gwamnati da ke garin Shagamu, a yayin da suke rike da wadannan makamai wadanda suka hada da wuka da adda a matsayin shaida. Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Ogun, CP Ikemefuna Okoye, ya aika da wasu manyan jami’an ‘yan sanda masu binciken kwakwaf daga hedikwatar rundunar da ke Eleweran a abeokuta domin binciken wannan al’amari, tare da daukar matakin da ya dace.
Kwamishinan ya yi yi kira ga iyaye da su kula da tarbiyar ‘ya’yansu yadda za ta dace da al’adunsu, amma ba koya wa yara miyagun al’adun wasu kasashen duniya ba. Ya tausayawa iyalan marigayi Charles Ajayi, musamman matarsa wacce ita ma lauya ce da ‘ya’yansu, inda ya bukaci su mika wannan al’amari ga Ubangiji.