dalibi ya zama mataimakin shugaban makarantar da yake karatu a Saudiyya

Wani dalibai ya zama mataimakin shugaban makarantar da yake karatu. Al’amarin ya auku ne a makarantar Ibn Sahrim da ke da nisan kilomita 50 a Yammacin Rafha, wani gari da ke Arewacin Saudiyya dab da kan iyakar kasar da Iraki. Shugaban makarantar ya dade ba shi da mataimaki, tun da aka fara zangon karatun wannan […]

dalibi ya zama mataimakin shugaban makarantar da yake karatu a Saudiyya
dalibi ya zama mataimakin shugaban makarantar da yake karatu a Saudiyya

Wani dalibai ya zama mataimakin shugaban makarantar da yake karatu. Al’amarin ya auku ne a makarantar Ibn Sahrim da ke da nisan kilomita 50 a Yammacin Rafha, wani gari da ke Arewacin Saudiyya dab da kan iyakar kasar da Iraki. Shugaban makarantar ya dade ba shi da mataimaki, tun da aka fara zangon karatun wannan shekarar, sai kawai ya rika tunanin yadda zai samu mafita.

Matimakin shugaban makarantar da ofishin gundumar ilimi ya turo makarantar, ya ce ba zai iya baro makarantar da yake aiki ba, domin babu wanda zai cike gurbinsa, kamar yadda jaridar Saudiyya ta Al-Watan ta ruwaito a Alhamis din da ta gabata.
Wannan makaranta ta Ibn Sahrim ta rubuta wa hukumar gundumar, inda ta roki a turo mata mataimakin shugaban makaranta.
Ganin cewa, bai samu amsa ba, sai shugaban makarantar ya yanke dauko daya daga cikin daliban makarantar ya dora masa alhakin gudanar da harkokin mulki a matsayin mataimakinsa. Ya kuma yanke wannan hukuncin ne bayan da ya tuntubi daliban makarantar. Don haka ya nada Hatem Al Shimmari, a matsdayin mataimakin shugaban makarant ana wucin gadi.
A wasikar da ya aike wa hukumar ilimi ta gundumar, shugaban makarantar ya ce ya dauki wannan matakin ne, don warware wasu matsaloli da ke tunkarar makarantar, bayan da mataimakin da aka nada mata ya ki zuwa, duk da cewa an ba shi mukami kimanin watanni hudu da suka wuce.
Shugaban makarantar ya ce Hatem zai taimaka masa a farkon lokacin karatu da kuma lokutan karatu cikin kwanakin aiki a mako mai zuwa.
Wannan yunkuri da shugaban makaranta ya yi, duk da cewa ba a saba ganin hakan ba, shi ma ya samu yabo daga masu mu’amala da kafofin sadarwa na intanet.
“Wannan hangen nesa ne mai matukar fa’ida, don haka ya kamata gundumar ilimi ta dauki tsarin ta rika aiwatyar da shi,” a cewar Sagane, wani mai shafi8n sadarwa.
“A hakikanin gaskiya ma ya kamata a rika amfani da shi a kwalejoji da jami’o’i, don tarbiyyantar da dalibai yadda ake shugabancin al’umma a cibiyoyin ilimin da ke kasar su. Sai dai abin takaici da yawa daga cikin irin wadannan cibiyoyin ilimi ba su himmatu wajen koyar da adalibansu a aikace ba. Ta yiwu wannan yunku8rin da makarantar Ibn sashrim ta bullo, shi ne irin san a farko, wajen tarbiyyantar da dalibaui dabarun shugabanci,” inji Sagane.