Dalibin da ya yi barci da na’urar sautin kunne ya zama kurma

Wani dalibin jami’a da ya kwanta barci yana sauraran wakoki ta hanyar amfani da na’urar sauti da ake makalawa a kunne ya tashi daga barcin ya zama kurma sakamakon kwanan da ya yi da na’urar manne a kunnensa. Binciken da likitoci suka yi na nuna cewa, sanadiyyar kwana da dalibin ya yi sanye da na’urar […]

Dalibin da ya yi barci da na’urar sautin kunne ya zama kurma

Wani dalibin jami’a da ya kwanta barci yana sauraran wakoki ta hanyar amfani da na’urar sauti da ake makalawa a kunne ya tashi daga barcin ya zama kurma sakamakon kwanan da ya yi da na’urar manne a kunnensa.

Binciken da likitoci suka yi na nuna cewa, sanadiyyar kwana da dalibin ya yi sanye da na’urar sauti na iya sa shi ya rasa jin sauti baki daya nan gaba.

Dalibin da ba a bayyana sunansa ba yana shekara ta biyu ce a Jami’ar Taiwan’s Asia Unibersity da ke kasar Taiwan. Dalibin yana karbar magani a asibitin Jami’ar Taiwan’s Asia da ke birnin Taichung.

Daraktan Tsangayar Cutar Kunne na Asibitin Dokta Tian Huiji ya gargadi jama’a su daina makala na’urar sauti a kunnnensu lokacin da za su yi barci.

Dokta Tian, ya kuma shawarci masu matsala irin wannan su tuntubi likita da wuri don magance cutar da wurin kafin cutar ta yi sanadiyyar kashe halittun jinsu.

Likitan ya ce, akwai hadari mutum ya wuni yana sanye da na’urar sauti a kunnensa sannan da daddare kuma ya ci gaba da sauraren na’urar a kunnensa, hakan zai iya janyo kurmancewa.

A yayin da Dokta Tian, yake tattaunawa da kafar labarai ta ‘OMG Taiwan’ ya ce, a lokacin da mutum ke barci jinin jikinsa bai cika zagayawa ba, kamar lokacin da ba ya barci. Wannan na nuna cewa, halittun gashin da ke cikin kunne suna samun zagayowar jini kadan wanda yake taimakawa wajen jin sauti mai karfi, ko ya mayar da mutum kurma.

A cewar masanin matsalar ciwon kunnen, sauraren na’urar sautin na da matukar hadari kasancewar na’urar na hana jin duk wani sauti, sai dai kawai sautin da mutum yake saurare da bai da wata hanyar fita sai mutum ya saurara.

A bara wani likita kuma Farfesa a Jami’ar New York Unibersity Langone a Amurka, William Shapiro, ya bayyana cewa, matasa ba su karbar shawarwari don haka suke lalata  jinsu sanadiyyar sauraran sauti mai kara ta hanyar amfani da na’urar da ake makalawa a kunne.

A watan Janairun bara, William, ya ce a duk cikin  matasa biyar daya na iya kamuwa da larurar rashin ji sanadiyyar karar sautin da yake saurare koyaushe.

 

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas