dalibin sakandare mai shekara 81 ya rasu
Wani dattijo mai shekara 81 mai suna Malam Muhammad Abubakar Modibbo, wanda kuma yake aji biyu a karamar Sakandaren Nazarin Larabci (SAS) ta Kano, ya rasu a shekaranjiya Laraba. Kamar yadda kafar sadarwa ta Premiun Times ta bayyana, an yi ittifakin cewa marigayin shi ne dalibin sakandare mafi yawan shekaru a Jihar Kano.Marigayi Modibbo a […]
Wani dattijo mai shekara 81 mai suna Malam Muhammad Abubakar Modibbo, wanda kuma yake aji biyu a karamar Sakandaren Nazarin Larabci (SAS) ta Kano, ya rasu a shekaranjiya Laraba.
Kamar yadda kafar sadarwa ta Premiun Times ta bayyana, an yi ittifakin cewa marigayin shi ne dalibin sakandare mafi yawan shekaru a Jihar Kano.
Marigayi Modibbo a lokacin yana raye kuduri aniyar ci gaba da karatu har sai ya samu digiri a jami’a.
Dattijon, wanda dan asalin Unguwar Yakasai ne a birnin Kano, ya shiga makarantar sakandare ne shekara biyu da suka gabata, bayan ya ci jarrabawar kammala karatun firamare ta Kundila a Kano.
daya daga cikin malaman makarantarsu, Abdulkarim Ibrahim ya bayyana dattijo Modibbo da cewa dalibi ne mai hazaka wanda ake jin dadin zama da shi a makarantar, domin kuwa yana dasawa tsakaninsa da dalibai da malamai. “Yana shirin daukar jarrabawa a badi. Bai samu cika burinsa na ci gaba da karatu zuwa jami’a ba, domin mutuwa ta dakile shi,” inji shi.