Daliget sun fara jefa kuri’a a zaben fid-da gwanin APC

Shugaban kwamitin zaben kuma Gwamnan jihar Kebbi Atiku Abubakar Bagudu Bagudu ya bayyana cewa daliget 2,340 za su yi zaben.

Daliget sun fara jefa kuri’a a zaben fid-da gwanin APC

Daliget sun fara jefa kuri’a a zaben fid-da gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.

An fara jefa kuri’a ne da misalin karfe 2 na dare a Dandalin Eagles Square da ke Abuja, bayan shugabannin jam’iyyar da manyan baki da ’yan takara su gabatar da jawabansu.

Ana gudanar da zaben ne a gaba jami’an Hukumar Zabe ta Kasar (INEC) da wakilan masu neman takarar da kuma shugabannin jam’iyyar da kuma jami’an tsaro.

Shugaban kwamitin zaben kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, ya ce mutum 14 ne za su fafata daga cikin masu neman tikitin su 23 a jam’iyyar.

Ya ce mutum tara daga cikin masu neman takarar sun janye kuma daliget 2,340 za su yi zaben.

Ya bukaci daliget din da su rubuta cikakken sunan dan takarar da suka zaba domin kada a samu rudani.

Ya bayyana cewa akwai mutun uku masu suna iri daya a cikin ’yan takara, kowannensu akwai Ahmed a cikin sunansa.

Mutane ukun su ne Bola Ahmed Tinubu da Ahmad Ibrahim Lawan da kuma Ahmad Sani Yerima.

A lokacin da suke jawabansu, ’yan takarar sun baje koli tare da tallata cancantarsu gami da dacewar daliget su zabe su.

Amma mutum bakwai daga cikinsu sun janye tare da mara wa Uban Jami’yyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu baya, suna masu bukatar daliget su zabe shi.

Mutum daya kuma ya janye wa Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, a yayin da sauran ’yan takarar kuma suka ci gaba da neman kuri’u.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya