Daliget ya raba wa jama’a miliyoyin da ’yan takara suka ba shi

Ya raba wa jama’a Naira miliyan bakwai da daliget suka ba shi, ya biya wa dalibai kudin jarabawa

Daliget ya raba wa jama’a miliyoyin da ’yan takara suka ba shi

Wani daliget a Jihar Kaduna, Rossi Tanko Sabo, ya raba wa al’ummarsa kudaden da masu neman takara suka ba shi gabanin zaben fitar da dan takara.

Rossi Tanko Sabo Rossi, wanda daliget ne a zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP wanda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya lashe,  ya raba Naira miliyan bakwai da ya samu ga talakawa a Karamar Hukumar Sango ta Jihar Kaduna.

Reuben Buhari, tsohon kakakin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Marigayi Patrick Yakowa, ya ce, Rossi, “Ya sayo kayan kwallo, ya biya kudin makaranta da kudin sabiti, sannan ya rabawa wa ragowar kudin ga kungiyoyin magoya baya.

“Ba maganar dacewa ko rashin dacewar karbar kudin da ya yi ake yi ba, saukinta shi ne ya sanya farin ciki a ran daruruwan talakawa. Madalla, Tanko,” inji Reuben Buhari.

Dansa daliget din, Tahir Tanko ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa mahaifin nasa ya yi alkawarin raba duk kudin da ya samu a zaben fitar da dan takara kashi biyu, domin daukar nauyin marayu da za su rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare.

Tahir ya ce mahaifina: “Mahaifina (Tanko Rossi Sabo) na daga cikin daliget din jam’iyyar PDP daga Jihar Kaduna kuma ya zama gagara-badau a yadda yake yin al’amurnasa.

“Ya kada kuri’a a zaben fitar da dan takarar Majalisar Dokokin Jiha da na Majalisar Wakilai da Sanata da gwamna da shugaban kasa.

“Tun kafin a yi zabukan ya yi alkawarin cewa duk kudin da ya samu a zabukan, tarawa zai yi, ya yi amfani da rabin kudaden wajen biyan kudin jarabawar WAEC da NECO.

“To albishirinku! Ya cika alkawarin, a gaya min wani wanda ya yi irin abin da mahaifina ya yi #TankoRossiSabo”